Ƙura ta lafa a Nahr Al-Bared na ƙasar Libanan | Labarai | DW | 05.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙura ta lafa a Nahr Al-Bared na ƙasar Libanan

Ƙura ta ɗan laffa a ƙasar Libanon bayanan an share daren jiya ana gwabra faɗa tsakanin dakarun gwamnati da mayaƙan ƙungiyar yan takifen Fatah Al-Islam.

Rahottani sun ce rundunar gwamnati, ta yiwa yan takifen ƙofar raggo, a kewayen matsugunan yan gudun hijira na Nahr Al-Bared, inda ɓangarori 2, ke ci gaba da bata kashi, a tsawan kwanaki 17.

Babban kommandan, na rundunra gwamnatin Libanon Jannar Michel Sleiman, ya sanar maneman labarai cewar za su ci gaba da kutsa kai a Nahr-Al Bared, har sai yan takifen sun bada kai bori ya hau.

A wani saban jawabi da ya gabatar, Praministan Libanon Fouad Siniora, ya sake zargin hukumomin Syria da hadasa wannan fitina, a matsayin martani, ga kotun ƙasa da ƙasa da Majalisar Ɗinkin Dunia ta girka domin shari´ar tsofan Praministan Libanon, Rafik Hariri.