Ƙungiyyar JEM ta Sudan ta kai sabbin hare-hare | Labarai | DW | 11.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyyar JEM ta Sudan ta kai sabbin hare-hare

Ƙungiyyar ´yan tawaye ta JEM a yankin Darfur na Sudan ta kai wasu sabbin hare-hare ga cibiyar haƙo mai dake ƙarƙashin ikon kamfanin ƙasar Sin a yankin Kordofan. Tuni ƙungiyyar ta JEM ta dawo da cibiyar haƙar man ƙarkashin ikonta. Matakin a cewar ´yan tawayen wata babbar alamace ta buƙatar kamfanin na Sin ficewa daga ƙasar. Rahotanni sun ce kamfanin na Sin na hako gangar mai dubu 35 ne akowace rana ta Allah ta´ala. ´Yan tawayen a cewar bayanai sun dauki matakin ne, bisa zargin cewa ƙasar sin na sayarwa da Gwamnatin Sudan makamai. Ire-iren waɗannan makamai a cewar ´yan tawayen da sune Gwamnati ke kai musu hare-hare. Ya zuwa yanzu dai babu wani bayani daya fito daga ɓangaren mahukuntan na Sudan, dangane da wannan sabon hari.