Ƙungiyoyin sa kai na baƙi a Jamus suna ƙara samun karɓuwa | Zamantakewa | DW | 23.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Ƙungiyoyin sa kai na baƙi a Jamus suna ƙara samun karɓuwa

To sai dai har yanzu ana nuna musu wariya a wasu wuraren

default

Wani malami Baturke yana taimakawa yaran baƙi a makaranta

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka, barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Taɓa Ka Lashe, shirin da ke duba batutuwan da suka shafi addinai, al´adu da kuma zamantakewa tsakanin al´umomi daban daban a wannan duniya ta mu.

Alƙalumma sun yi nuni da cewa mutane kimanin miliyan 23 ne a nan Jamus suke tafiyar da ayyukan irin na yiwa jama´a hidima. Daga cikin baƙi kuwa kusan kashi ɗaya cikin huɗu suna aiki gadan gadan a cikin ƙungiyoyin iri daban daban na taimakon jama´a a unguwanni da garuruwa. Wani nazari da ma´aikatar ili ta tarayyar Jamus ta yi yayi nuni da cewa da yawa daga cikin ƙungiyoyin sa kai na baƙi a cikin ƙasar suna tafiyar da aiki na taimakawa jama´a, to amma ba a ba su damar shiga cikin kungiyoyi na Jamusawa. A saboda haka bakin suke haɗa kai wuri guda don taimakawa juna musamman ganin cewa matsalolin iri daya suke fuskanta kana kuma bukatunsu kusan iri ɗaya ne. To shirin na yau zai duba ayyukan irin waɗannan ƙungiyoyi da kuma rawar da suke takawa wajen kyautata zamantakewa tsakanin baƙi da ´yan ƙasa haɗe da matsalolin da suke fuskanta wajen tafiyar da wadannan ayyuka. Masu sauraro Mohammad Nasiru Auwal ke lale marhabin da saduwa da ku a wannan lokaci.

Selma Öfkeli ´yar asalin ƙasar Turkiya tana daya daga cikin masu tafiyar da aikin taimakawa jama´a. Ta yi nuni da cewa tana alfahari da wannan aiki da take yi musamman na taimakawa tsofaffai, sannan sai ta ƙara da cewa.

Öfkeli:

“Ba zaka sama wanda ba ka sanshi ba ko ba ka taba ganinshi ba karar tsana ba. Dole sai kun san juna tukuna. A game da aiki na kuma, gaskiya ina jin daɗinsa musamman a duk lokacin da zan kaiwa tsofaffin ziyara, kamar Madam Krikos, wadda a kullum na ke sha´awar kai mata ziyara.”

Tun sama da shekaru biyu Selma Öfkeli take kaiwa Madam Krikos mai shekaru 82 kuma ba ta iya tashi, ziyara a kai a kai tana kula da ita. Öfkeli tana daga cikin mutane kalilan masu asali da ƙasashen ƙetare dake yiwa jama´a hidima don raɗin kansu. Har halin da ake ciki ba dukkan baki a wannan ƙasa suke sha´awar yin irin wannan aiki ba, bisa dalilai na jahiltar aikin yayin da waɗanda ke yin sa kuma ba a ganinsu da wata daraja, inji Selma Öfkeli sannan sai ta ƙara da cewa.

Öfkeli:

“Ra´ayin da yawa daga cikin mu shi ne bai kamata ka kaiwa wani bako wanda ba ka sanshi ba ziyara. Tambayar da wasu ke yi ita ce mai ya sa za su ziyarci mutanen da ba su sansu ba? Shin me za su iya ba su? A nan ina kira a gare su da su yi ƙoƙari su fara, sannan ne za su ga irin fa´idar da ke cikin wannnan aiki na yiwa jama´a hidima.”

Rashin ɗaukar wannan batu da muhimmanci a tsakanin al´ummomin wannan ƙasa masu asali da kasashen ƙetare na da nasaba da fahimtar da suka yiwa aikin na sa kai ko yiwa jama´a hidima don radin kai. Arif Ünal shugaban sashen kula da baƙi na cibiyar kiwon lafiya ta birnin Kolon, masani ne na irin damuwar da masu aikin sa kai ke nunawa. Ya ce rashin iya yaren na daga cikin abubuwan da ke kawo ciƙas. Amma kuma da akwai wasu dalilan, inji Arif Ünal sannan sai ya ci gaba da bayani yana mai cewa.

Ünal:

“A iya fahimtar mu, aikin sa kai bai da wani muhimmanci ga baƙi musamman ´yan asalin kasar Turkiya dake a wannan ƙasa. Dalili kuwa shi ne tun a ƙasashensu ba su saba da irin wannan aiki ba.”

Wani binciken jin ra´ayin jama´a da ma´aikatar ilimi ta tarayyar ta yi ya gano cewa da yawa daga cikin masu aikin sa kai ko yiwa jama´a hidima sun fi ƙarfi a ɓangaren ƙungiyoyi na addini da na yada al´adu, sai kuma na matasa da na siyasa. Ganin cewa addini da al´adu sun fi ɗaukar hankalin masu aikin sa kai, hakan ya samo asali musamman dangane da taimakon juna da ake yi a ire-iren waɗannan ƙungiyoyi. Wata da ake kira Emine Sen ta yi nuni da cewa addini ya taka muhimmiyar rawa ga shawarar da ta yanke na shiga aikin sa kai gadan-gadan a wani masallaci, inda a kullum take kula da batutuwan da suka shafi mata. Ta ce ba a ba ta damar shiga ƙungiyoyin sa kai na Jamusawa ba.

Sen:

“Ba mu san abubuwa da yawa ba. Alal misali ba mu san ƙungiyoyi da dama ba, ba mu san ofisoshinsu ba ko wanda zamu iya tuntuɓa idan muna neman wani bayani game da su ba. Akwai abubuwa da dama da ya kamata a yi bayaninsu musamman dangane da taimakon da ya kamata a bayar. Amma duk da haka ana rashin wata kafa ta tuntuɓar juna.”

To amma ra´ayin Cengiz Iyirli wanda shi ma yake aikin sa kai, ya bambamta da na Emine Sen.

Iyirli:

“Na tashi ne a wani gidan al´adu a Turkiya. A nan na koyi abubuwa da dama kamar rera waƙoƙi, rawa, rubuta adabi da zane. Da na nunawa shugaban wannan kungiya abubuwan da na nakalta, sai ya bari muka buɗe sashen yada al´adu. Kuma yanzu haka ni na ke kula da wannan sashen.”

Tun fiye da shekaru 40 kenan Cengiz Iyirli, mai shekaru 74 a duniya ya ke nan Jamus kuma yake aikin sa kai a cikin wata ƙungiya mai zaman kanta dake birnin Kolon. Kungiyar da ake kira Labour Welfare ta shafe fiye da shekaru 40 tana haɗin guiwa da ƙungiyoyin baki. A kullum wannan kungiya ta Jamusawa tana inganta aikin taimakon da take yiwa baƙi, inji Birgit Yagusch ta hadaddiyar ƙungiyar sa kai ta tarayyar Jamus.

Yagusch:

“Ko da yake muna ƙoƙarin faɗaɗa aikinmu, amma saboda rashin wani ingantaccen tsari na shigar da baƙin musamman ba su damar faɗa a ji, ya sa ana fuskantar ƙarancin baƙi da ke sha´awar sadaukar da lokutansu don yiwa jama´a hidima.”

Yagusch ta ce duk da kyakkyawar aniyar wasu baƙin na yin aikin sa kai amma akwai wasu abubuwa masu tarin yawa dake hana ruwa gudu. Ta yi watsi da damuwar da ake nunawa cewa aikin sa kai a tsakanin bakin, idan ya kai wani lokaci yana iya haddasa matsaloli na zamantakewa.

Yagusch:

“A halin da ake ciki mun tabbatar da cewa aikin sa kai na kungiyoyin baki yana kara yin kyakkyawan tasiri a tsakanin Jamusawa. To sai dai ina ganin muhimmin abu shi ne ya kamata a kara samun taimako daga ɓangaren ´yan siyasa don tinkarar wannan ƙalubale kafin ya zama gagarabadau.”