Ƙungiyoyin Falasɗinawa na Hamas da Fatah sun haramta wa al’ummansu yawo da makamai. | Labarai | DW | 10.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyoyin Falasɗinawa na Hamas da Fatah sun haramta wa al’ummansu yawo da makamai.

A wata sabuwa kuma, Ƙungiyar Hamas da ke jagorancin hukumar Falasɗinawa da Ƙungiyar Fatah ta shugaban Falasɗinawan Mahmoud Abbas, sun cim ma yarjejeniyar haramta wa al’umman Falasɗinun yawo da makamai. Ɓangarorin biyu sun ba da sanarwar hakan ne, bayan wani taron gaggawa da suka yi, da nufin kawo ƙarshen musayar wutar da dakarunsu suka yi ta yi da juna tun ran litinin da ta wuce. Kawo yanzu dai rahotanni sun ce, fiye da mutane 10 ne suka ji rauni, a wata karawar da dakarun ɓangarorin biyu suka yi da juna jiya talata. A kudancin zirin Gaza kuma, rahotannin sun ce mutane 3 ne suka rasa rayukansu a fafatawar da ’yan ta kifen ƙungiyoyin Hamas da na Fatah suka yi da juna a ranar litinin.