Ƙungiyoyin agaji sun ce yawan baƙin hauren da suka rasa rayukansu a tsibirin Canaries na ƙara haɓaka. | Labarai | DW | 31.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyoyin agaji sun ce yawan baƙin hauren da suka rasa rayukansu a tsibirin Canaries na ƙara haɓaka.

Ƙungiyoyin ba da taimamkon agaji sun ce yawan baƙin hauren da suka rasa rayukansu, a yunƙurinsu na isa tsibirin Canaries a ƙarshen makon da ya gabata, ya ƙara haɓaka. Kawo yanzu dai rahotanni na nuna cewa an tsamo gawawwaki 84 na baƙin hauren daga teku, yayin da har ila yau ba a san makomar wasu baƙin hauren guda 50 ba tukuna. A ran asabar da ta wuce ne, wasu jiragen ruwa ɗauke da baƙin haure daga Murteniya suka nitse a gaɓar tekun tsibirin Canaries, yayin da tsakanin jiya da yau kuma aka kame wasu ɗari biyu da hamsin, waɗanda ke yunƙurin isa a tsibirin. Ƙasar Spain, mai mallakar tsibiran na Canaries, ta yi kira ga Ƙungiyar EU da ta tallafa mata, wajen shawo kan ambaliyar baƙin hauren da take huskanta.