1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ƙungiyarr EU ta dakatad yunƙurin sasantawa da take yi tsakanin Turkiyya da Cyprus.

Bayan dakatad da shirin sasantawa tsakanin Turkiyya da ƙasar Cyprus da ƙungiyar EU ta yi, masharhanta na ganin cewa, shwawarin da ake yi kan shigar Turkiyya cikin ƙungiyar ma na huskantar wargajewa.

Tutocin Turkiyya da na Ƙungiyar EU

Tutocin Turkiyya da na Ƙungiyar EU

Da yake bayyana wa maneman labarai dalilan da suka janyo dakatad da shirin shiga tsakanin a birnin Helsinki, ministan harkokin wajen ƙasar Finnland, Erkki Tuomioja, ya ce duk yunƙurin da aka yi na shawo kan ɓangarorin biyu su zauna kan teburin shawarwari ya ci tura.

Duk ɓangarorin biyu dai, wato Girka da Turkiyya, sun yi ta zargin juna da janyo wargajewar shawarwarin ministocinn harkokin wajensu, da aka shirya yi a birnin Helsinki a ƙarshen wannan makon. Tuni dai, Firamiyan Turkiyyan, Tayyip Erdogan, ya ce ƙungiyar ta EU, ba ta da alamun iya sasanta rikicin da ke tsakanin ƙasarsa da Cyprus ɗin. A nasa ganin dai, wannan batun ya fi ƙarfin EUn. Sai Majalisar Ɗinkin Duniya ce za ta iya tinkarar matsalar don warware ta. Ƙasar Finnland dai, wadda ke jagorancin ƙungiyar EUn a halin yanzu, ta shawarci Turkiyyan da ta janye dakarunta daga garin Famagusta, mai tashar jirgin ruwa, a yankin Turkawa na arewacin tsibirin na Cyprus. Idan hakan ya samu, za a buɗe wa Turakawan tsibirin tashar jirgin ruwan, don su iya tafiyad da harkokin cinikayyarsu. Har ila yau dai, ana bukatar Turkiyyan kuma ta buɗe wasu daga tashoshin jiragen ruwa da filayen jiragen samanta ga jiragen Cyprus.

Tsibirin na Cyprus dai, wanda ke rabe tun fiye da shekaru 30 da suka wuce, ya sami shiga cikin ƙungiyar EUn ne a cikin shekara ta 2004. Amma a ɓangaren Girkawa na tsibirin ne kawai, ake aiwatad da ƙa’idojin da dokokin ƙungiyar.

Turkiyya dai har ila yau, ta ƙi amincewa da wanzuwar yankin kudancin tsibirin tamkar ƙasa mai cin gashin kanta. Firamiyan Girka, Konstantin Karamanlis, ya sake sukar wannan matsayin da Turkiyyan ta ɗauka. Sabili da haka ne ma, ya ƙi tura ministan harkokin wajensa zuwa taron da aka shirya yi a birnin Helsinki a ƙarshen wannan makon. Da yake mai martani, Firamiya Erdogan na Turkiyya, ya ce babban kuskure ne a angaza wa ƙasarsa kan wannan batun. Yana kuwa matashiya ne da wa’adin da ƙungiyar EUn ta bai wa ƙasarsa na ta buɗe tashoshin jiragen ruwa da na samanta ga jiragen Cyprus ɗin kafin ƙarshen wannan shekarar. Ita dai EUn ta ce idan hakan bai samu ba, za ta dakatad da tattaunawar da take yi da Turkiyyan kan shigarta cikin ƙungiyar. Bisa ƙa’ida dai, ko wace ƙasar ƙungiyar, wato har da Cyprus ɗin ma ke nan, za ta iya hawar kujerar na ƙi don hana ci gaban tattaunawar da Turkiyya.

A ganin ita Turkiyyan dai, rikicin Cyprus, ba shi da wata jiɓinta da neman shiga ƙungiyar EUn da take yi. Amma jami’an ƙungiyar na watsi da wannan hangen nata, inda suke bayyana cewa duk wani mai son shiga wata ƙungiya, to kamata ya yi, ya san ko su wane ne ’ya’yanta. Shi ko ministan harkokin wajen Finnland, Erkki Tuomioja, cewa ya yi, duk da cikas ɗin da aka samu a yanzu, zai ci gaba da neman hanyoyin cim ma wata madafa don samo bakin zaren warware wannan rikicin.

Sai dai jami’an diplomasiyyan ƙungiyar na ganin, matsalar ba haka kawai za a iya warware ta ba, saboda ko a cikin zauren shawarwari ɗaya ma, ɓangarorin biyu sun ƙi su zauna tare. Masharhanta dai na ganin cewa, watakila shugabannin ƙasashen ƙungiyar ne za su tinkari warware wannan matsalar, a taron ƙolin da za su yi a cikin watan Disamba mai zuwa.

A yau ne dai ministan harkokin wajen Finnland ɗin, zai sadu da wakilan al’umman Turkawa na arewacin tsiibirin na Cyprus, Mehmet Ali Talat, duk da wannan koma bayan da aka samu. Kwanakin bayan nan ne dai Talat ya yi suka ga ƙungiyar EUn da cewa ta da gangan take ƙin ɗage takunkumin saniyar ware da ake yi wa yankin arewacin tsibirin. A halin yanzu dai, tsibirin na nan ne kamar ƙasashe biyu, wato yankin Girkawa a kudu da kuma yankin Turkawa a arewa. Wata faufutukar da aka yi ta cim ma haɗe tsibirin a cikin shekara ta 2004, dab da shigar yankin Girkawan cikin ƙungiyar EU, ya ci tura ne saboda daddagewa shirin da su Girkawan tsibirin suka yi.

 • Kwanan wata 03.11.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtxY
 • Kwanan wata 03.11.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtxY