Ƙungiyar tawayen JEM a Sudan ta zargi gwamnati da hallaka fara hulla 17 | Labarai | DW | 21.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyar tawayen JEM a Sudan ta zargi gwamnati da hallaka fara hulla 17

Ƙungiyar tawayen JEM, dake yankin Darfur na ƙasar Sudan, ta zargi sojojin gwamnati, ta yi mata luggudan wuta, tare da hallaka fara hulla 17, wanda ba su ci kasuwa ba, rufa ta faɗa kan su.

A cewar shugaban rundunar tawayen,Khalil Ibrahim, a duk tsawan ranekun juma´a da assabar, dakarun gwamnatin Kahrtum, sun yi ta shawagi, da jiragen sama a sararin samaniyar Darfur , su ka kuma cilla bama-bamai, da burin hana taron da ƙungiyoyin tawaye su ka tsara, da burin samar da hadin kai kamin haɗuwa da tawagar gwamnati.

Saidai ya zuwa yanzu, hukumomin Khartum ba su ce ƙalla ba, a game da wannan zargi.