Ƙungiyar tawayen FN a Cote d´ivoire ta ƙauracewa tantanawar kwance makamai | Labarai | DW | 08.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyar tawayen FN a Cote d´ivoire ta ƙauracewa tantanawar kwance makamai

Shugaban rundunar tawayen Cote d´Ivoire, Guillaume Soro, ya kiri taron manema labarai yau, a birnin Bouake.

Guillaume Soro, ya bayyana ƙauracewa rundunar FN, daga tantnanawar da ake ta kwance ɗamara yaki.

Ya ɗauki wannan mkataki, domin nuna adawa da yadda a cewar sa, shugaba Lauran Bagbo, ya yawaita kalamomi na tsokanar faɗa.

A jawabin da ya gabatar lahadin da ta wuce, albarkacin ranar samun yancin kan ƙasar, Lauran Bagbo, ya bayana rijistan masu zaɓe, da ake a halin yanzu , a matsayin wani mataki, wanda ba zai ba mutum, damar samun takardar zama ɗan ƙasa ba, kazalika ya ce, ba za shi sauka daga mulki ba, sai lokacin da aka shirya zaɓen shugaban ƙasa.

Bisa tsarin Majalisar Ɗinkin Dunia,a ƙarshen watan oktober mai zuwa ne, ta kamata, Lauran Bagbo ya sauka daga mukami.

A cikin taron manema labaran na yau, Guillaume Sorro ya buƙaci girka rundunar haɗin gwiwa, wace Praministan riƙwan ƙwarya zai dogaro kanta.

Guillaume Sorro ya ce a yanzu yan tawaye sun ɗauki Lauran Bagbo, a matsayin shugaba rundunar tawaye, kuma Praminista Charles Konnan Banny kaɗai, ke matsayin abokin tantannawa