Ƙungiyar taraiyar Afirka a Darfur ta mika jagaronci ga rundunar Majalisar Ɗinkin Duniya | Labarai | DW | 31.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyar taraiyar Afirka a Darfur ta mika jagaronci ga rundunar Majalisar Ɗinkin Duniya

Ƙungiyar Taraiyar Afirka a lardin Darfur ta miƙa ragamar jagorancin dakarun wanzar da zaman lafiya na haɗin gwaiwa tsakanin AU da Majalisar Ɗinkin Duniya wadda ake ganin zai tabbatar da zaman lafiya a yankin da yaƙi ya tagaiyara. Bikin miƙa harkokin zaman lafiyar a yankin Al Fasher ya zo ne bayan watanni na matsin lamban kasashen duniya kan shugaba Omar Al Bashir da ya amince da tura dakarun. Rundunar ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Darfur da za a kira ta da suna UNAMID itace zata zamo runduna mafi girma da majalisar ta taɓa turawa kowace kasa inda zata ƙunshi dakarun soji 20,000 da ‘yan sanda 6,000 da farar hula. Ya zuwa yanzu dai tuni sojoi da ‘yan sanda kusan 9,000 sun isa lardin na Darfur.