ƙungiyar RCD a jahuriya Demokradiyar Kongo ta bayyana shiga zaɓe mai zuwa | Labarai | DW | 25.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ƙungiyar RCD a jahuriya Demokradiyar Kongo ta bayyana shiga zaɓe mai zuwa

Ƙungiyar tawayen RCD, ta Jamhuriya Demokaraɗiyar Kongo, mai samun goyan baya, daga ƙasar Rwanda, ta bayyana shiga zaɓe shugaban ƙasa, da na yan majalisun dokoki, da za a yi ,ranar 18 ga watan juni mai zuwa.

Ƙungiya,r da ta rikiɗa zuwa jam´iyar siyasa, ta bayyana wannan sanarwa a yammancin jiya, a cibiyar ta dake birnin Kinshasa.

Shugabann ƙungiyar Azarias Ruberwa, bugu da ƙari ɗaya daga mataimakan shugaban ƙasa 4, ya bayyana ajje takara a wannan zaɓe.

Da farko RCD, ta yanke shawara ƙauracewa zaɓen, muddun ba a cika, wasu sharuɗɗa, da ta gindaya ba.

A jawabin da yayi ranar 16 ga watan da mu ke ciki, shugaban ƙasa Lauran kabila, yayi alkawarin biyan buƙatocin tsafin yan tawayen.

A ɗaya hannun, sanarwar ta RCD, ta yaba shiga tsakanin da ƙasashe da kuma ƙungiyin ƙasa da ƙasa, su ka yi, ta fannin samar da zaman lahia, a jamhuriya Demokraɗiyar Kongo.

Saidai, a yayin da RCD ta bayyana shiga zaɓen, a yankin Ituri, a na cigaba da gwabaza faɗa, tsakanin yan tawaye da dakatrun gwamnati, tare da haɗin gwiwar dakarun majalisar Ɗinkin ɗunia.