1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Ƙungiyar mata ta Womnet a Marokko

Ƙungiyar tana taimakawa mata wajen neman ´yancinsu

default

Sabuwar dokar iyali a Marokko

An gano a wani taron mata da aka gudanar a nan Bonn ‚yan makonnin baya, cewar har yanzu dai da sauran aiki a gaba, idan har ana son a cimma dai daituwa tsakannin maza da mata a fannin rayuwa na yau da kulun. Mahallarta a wannan taro wanda wata ƙungiya mai suna Womnetwork ta shirya domin tattauna matsaloli da mata ke fuskanta a harkokin yau da kulun, sun ce har yanzu dai da rina a kaba, amma kuma an samu ci gaba a wasu ƙasashe kamarsu Moroko wadda ta ƙirƙiro da wata doka ta kyautatawa iyali.

Assalamun Alaikum, Rabi Abubakar Gwandu ke murnar kasancewa tare da ku a filin Abunamau magannin a kwaɓe mu na wannan mako.

Wannan sabuwar doka da mahukuntar ƙasar Moroko suka sanya hannu kanta a shekara ta 2004, ta samu karbuwa da hannu biyu biyu ga al'umaar wannan kasa inda Musulmi suke da rinjaye. Dokar kuma wadda ke ƙumshe da canje canje kann harkokin da suka jiɓinji gado, aure da hakokkin yara, ya kawo cece kuce tsakannin mazan wannan ƙasa kafin majalisa ta amince da ita, bayan sa hannun sarki. Rabea Naciri memeba ce ta wata ƙungiya dake fafutukar ‚yancin mata a fanni na dimmokraɗɗiyya, tace ba ƙaramin gwagwarmaya suka yi kafin su cimma wannan biyan bukata ba.

A lokacin da muke gwagwarmayar neman an ɗoki matakan da suka dace kann dokokin da suka shafi hakkoƙin mata, jama'a sun ɗauki batun aiwatar da canji ga dokokin tamkar kamar aikata wani abu na saɓo. ‚Yan siyasa, da malamai masu ra'ayin mazan jiya, kana da mutanen karkara, sun fi bada ƙarfi kann dokokinmu wadanda muka gada. A lokacin dai mata da maza musanman marassa ilimin boko sun nuna biyayya ga tsohuwar dokar kamar yadda suka amince da alkur'ani mai girma. Sun kuma ɗauki batun tamkar dai dai da kyeta dokokin addini. Ya ɗauke mu shekaru ashiri kafin mu cimma nasara. Shekaru ashirin na gwagwarmaya.

A ƙarshe dai mata sun cimma nasara kann wannan mataki. Kafin shekara ta 2004, dokokin Moroko bata baiwa mace damar sanya hannu kann takardar shaidar aure ba, idan har zaka yi haka, sai tare da amincewa kana da rakiyar wani magabata ko kuma mahaifinta. Amma duk da cewar yanzu wadannan ka'idoji sun zama tarihi, Naciri tace wasu mata har yanzu na ja da baya wajen ɗaukan wasu matakai bisa raɗin kansu.

Da farkon farin, a shekarun 2004 da 2005 mata sukan nuna fargaba wajen amfani da damar da wannan sabuwar doka ta basu, amma kuma bisa ga rahotannin da ma'aikatar kula da harkokin shari'a ta fitar a shekara ta 2007, an samu ƙaruwa a yawan matan da suka aure tare da hallartar ɗaurin aurensu ba tare da sun nemi amincewa daga mahaifansu ba kamar yadda abin yake ada. Wannan wata cigaba ce mai faranta zuciya. Kuma hakan yasa nike cewa doka tana da ikon aiwatar da canje canje a kann rayuwar yau da kulun na al'uma. Ba gaskiya bace cewa dokoki basa taka muhinmiyar rawa kann harkokin rayuwa na yau da kulun. Mun ga sakamakon wadannan canje canje a fanning rayuwa nay au da kulum ga jam'ar ƙasar Morroko.

Yanzu haka matan Morroko sun fara shiga ana damawa dasu a harkokin siyasa, da dama daga cikinsu sun samu muƙamai cikin gwamnati kana suna taka rawar gani a fannin siyasa kamar takwarorinsu maza.

Ko da yake ana biyayya ga wadannan sabbin dokoki da suka baiwa mace ‚yancin ta, Amma har yanzu akwai sauran aiki a gaba idan ana son a ci cikakkiyar gajiyar wannan doka musanman kann ‚yamcin mace wajen kashe aurenta. Inji Naciri.

Wannan doka dai an kafa ta da bin ka'idojin da Allah (SWT) Ya tsara mana cikin al'kurani mai tsarki, shi yasa ko da da wani da ke da ta cewa kann ta, baya saurin buɗe bakinsa, kuma dole ne ya yi biyayya da ita.