Ƙungiyar Hizbullah ta yi ikirarin kai harin rokoki a garin Nahariya da ke arewacin Isra’ila. | Labarai | DW | 13.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyar Hizbullah ta yi ikirarin kai harin rokoki a garin Nahariya da ke arewacin Isra’ila.

Ƙungiyar Hizbullah, da ke yaƙan dakarun Isra’ilan a kudancin Lebanon, ta ce ita ta kai harin rokokin da suka faɗo a garin Nahariya da ke arewacin Lebanon. Tun jiya laraba ne dai ake ta ba ta kashi a yankin kudancin Lebanon ɗin, bayan da dakarun Hizbulllahin suka suka kai hari kan wani rukunin tsaron iyaka na rundunar sojin Isra’ilan a kwanaki biyu da suka wuce, inda suka kame mata sojoji biyu, sa’annan kuma suka kashe wasu guda 8.

Rahotannin da ke iso mana sun ce, a halin yanzu, babu kowa a kan titunan garin Nahariyan. Mafi yawan jama’a sun bi umarnin ’yan sanda sun fake a cikin ramukan ƙarƙashin ƙasa, don kar kansu.