Ƙungiyar EU da IMF za su talaffawa Ireland | Labarai | DW | 22.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyar EU da IMF za su talaffawa Ireland

Ireland ta amince da karɓar agajin rancen euro biliyan 90 domin tada komaɗar tattalin arzikinta

default

Brian Cowen

Ƙungiyar Tarayya Turai da asusun ba da lamuni na Duniya sun ce, a shirye su ke su tallafawa ƙasar Ireland da rancen da ya kai ƙudin euro dala biliyan 80 zuwa 90 domin agaza ma tsarin tattalin arziki na ƙasar da ke cikin wani halin tsaka mai wuya.

Hakan kuwa ya biyo bayan buƙatar da hukumomin kasar suka fito fili suka bayyana, abin da kuma ya janyo fushin al 'umar dangane da abinda suka kira abin kunya.

To sai dai Priministan Ireland Brian Cowen ya kare gwamnatinsa akan wannan yunkuri da ya ce ya zama tilas.

"Ina iya tabbatar da cewa gwamnatinmu a yau ta amince da karɓar wannan tallafi na ƙungiyar Tarayyar Turai, bayan da suka amince da bukatarmu. Kuma nan gaba za a shiga tattaunawa domin samun agajin".

A jiya  lahadi dai wasu Jama'ar a ƙasar ta Ireland sun gudanar da zanga-zanga domin yin Allah wadai da matakin da gwamnatin ta ɗauka.

Mawallafi :Abdurahamane Hassane

Edita        : Zainab mohammed Abubakar