Ƙungiyar AU ta ce an kashe sojojinta biyu a yankin Darfur. | Labarai | DW | 20.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyar AU ta ce an kashe sojojinta biyu a yankin Darfur.

Ƙungiyar Tarayyar Afirka, wato AU, ta ce dakarun kare zaman lafiyanta biyu sun rasa rayukansu, a wani kwanton ɓaunar da ’yan tawaye suka yi wa ayarin motocinsu a yankin Darfur na ƙasar Sudan. Duk da yarjejeniyar zaman lafiyar da da aka cim ma tsakanin gwamnatin Sudan da ɗaya kungiyar ’yan tawayen a cikin watan Mayun da ya gabata, ana ta samun haɓakar tashe-tashen hankulla a yankin. Ƙungiyar AUn ta ce an kai wa dakarun kare zaman lafiyan hari ne, a wani yankin da ke hannun ƙungiyoyin ’yan tawayen da suka ƙi sanya hhannu kan yarjejeniyar samad da zaman lafiyar, sai dai ta kuma ce har ila yau, ba a gano asalin waɗanda suka kai wannan harin ba tukuna.

Tun da rikici ya ɓarke a yankin na Darfur a cikin shekara ta 2003, dubban mutane ne suka rasa rayukansu, sa’annan wasu miliyan biyu da rabi kuma suka yi asarar matsugunansu.