Ƙungiyar agaji ta Islamic Relief | Zamantakewa | DW | 26.06.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Ƙungiyar agaji ta Islamic Relief

Ƙungiyar tana taimakawa a yankunan da ake fama da rigingimu da yaƙe-yaƙe.

default

Fari da matsalar abinci a Ethiopia

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka, barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Taɓa Ka Lashe, shirin da ke duba batutuwan da suka shafi addinai, al´adu da kuma zamantakewa tsakanin al´umomi daban daban a wannan duniya ta mu.

Matsananciyar yunwar da ta addabi ƙasashen Sudan da Ethiopia a cikin shekara ta 1984 ta tayar da hankalin duniya baki ɗaya. A dangane da wannan bala´i na yunwa wani likita da ake kira Hany El Banna dake birnin Birmingham na ƙasar Ingila ya fara shirya taimakon jin ƙai na na farko ga miliyoyin mutanen da suka shiga halin Laha´ula´i a waɗannan ƙasashen Afirka. Ta haka aka kafa wata ƙungiyar agaji ta musulmi mai suna Islamic Relief. A cikin shekaru ƙalilan da kafuwarta wannan ƙungiya ta faɗaɗa ayyukanta ya zuwa na ƙasa da ƙasa inda ta kafa rassa da yawa a ko wane yankin na wannan duniya ta mu. A halin da ake ciki yanzu ƙungiyar ta Islamic Relief ta na da wuraren tafiyar da ayyukanta da tara kayakin agaji a ƙasashen Turai 11. To shirin Taɓa ka lashe na wannan makon zai gabatar da wannan ƙungiya ce wadda ke ba da taimako a yankunan da ake fama da rigingimu da yaƙe-yaƙe.

Madalla. Ko da yake ƙungiyar ta Islamic Relief ta fi samun kuɗin tafiyar da ayyukanta daga taimako da take samu daga musulmi. Tarek Abdel-Alem haifaffan ƙasar Masar ya shafe sama da shekaru 20 a nan Jamus. Yanzu dai shi ne shugaban reshen ƙungiyar a nan Jamus. Tun dai a shekarar 1996 ƙungiyar ta kafa hedkwatarta a birnin Kolon. Tarek Abdel-Alem yayi bayanin ayyukan ƙungiyar yana mai cewa.

“Muna aiki ne a matsayin wata haɗaɗɗiyar ƙungiya. Hedkwatar mu dai a birnin Birmingham na ƙasar Ingila ta ke. Amma ko wane ofis a cikin ƙungiyar ta Islamic Relief na aiwartar da dubarun raɗin kansa da suka shafi tara kuɗaɗen taimako kamar yadda dokokin ƙasar da ya ke ciki suka tanadar.”

Ayyukan agaji kamar rarraba kayan abinci da magunguna da sauran aikin agaji kamar samar da tsabtattacen ruwan sha ga jama´a a yankunan da ake fama da rikice rikice shi ne abin da ƙungiyar ta sa a gaba. To sai dai ban da wannan ƙungiyar tana ba da taimakon sake gina yankuna musamman bayan aukuwar bala´o´i daga Indallahi ko yaƙe yaƙe, inda a halin yanzu take ba da agaji a ƙasashe 26 a wannan duniya ta mu. Daga cikin waɗannan ƙasashen kuwa har da Bosniya-Herzegovina, Afghanistan, Albaniya, Falasɗinu da kuma Kenya. A nan Jamus ma ba a bar ta a baya wajen agazawa ba, inda alal misali ta taimaka da kuɗi euro dubu 30 wajen sake gina garin Pirma dake kusa da birnin Dresden bayan wata ambaliyar ruwa da ta auku a yankin a shekara ta 2002. Shugaban reshen ƙungiyar a Jamus Tarek Abdel-Alem ya ce ƙungiyar ta fi samun mafi yawa na kuɗaɗen taimakonta daga ƙasashen Turai.

Ya ce “Muna samun taimakon ne daga musulmi mazauna ƙasashen nan nahiyar Turai. Ban da taimako daga mutane masu zaman kansu, muna kuma samun taimako daga majalisar ɗinkin duniya da kuma ƙungiyar jin ƙai ta Humanitarian Aid Department, wadda ke ƙarƙashin ƙungiyar tarayyar Turai EU.”

Abdel-Alem ya yi nuni da cewa kalmar Islam dake haɗe da sunan ƙungiyar na da nasaba da al´adu fiye da wasu dalilai na addini, sannan sai ya ƙara da cewa.

“Ƙungiyar Islamic Relief ba ƙungiyar addini ba ce, a´a ƙungiyar jin ƙai ce da ke aiki ƙarƙashin dokokin addinin musulunci. Wato abin nufi shi ne dukkan musulmin da ke son ba da zakka suna iya ba mu. A haƙiƙanen gaskiya kuɗin zakka ya kai kashi 20 zuwa 25 cikin 100 na kuɗaɗen taimakon da ƙungiyar ke samu. Muna samun mafi yawa na kuɗaɗen mu daga masu ba da taimako don agazawa mutanen da ke fama da matsananciyar yunwa sai kuma masu tallafawa aikace aikacen da muke gabatarwa.”

A shekara ta 2007 ƙungiyar ta samu kuɗin taimakon da a kai euro miliyan 3 da dubu 600. A nata ɓangaren tana taimakawa dukkan al´umma ba wai musulmi kaɗai ba, a´a duk wani mabuƙaci na samun taimakonta ba tare da la´akari da addininsa ko ƙabilansa ko jinsi sa ba. Hasali ma dai wannan shi ne dalilin da ya sa reshen ƙungiyar Islamic Relief a Jamus ya zama wata ƙungiyar musulmi ta farko da aka ɗauke ta a cikin haɗaɗɗiyar ƙungiyoyin agaji masu zaman kansu a Jamus wato VENRO. Shugaban VENRO Peter Runge ya yi ƙarin bayani yana mai cewa.

“Muhimmin batu dangane da taimakon jin ƙai shi ne a yi ƙoƙarin sauƙaƙawa ko magance raɗaɗin wahalar da mutum ke fama da shi. A iya sani na kam ƙungiyar Islamic Relief ta cike wannan ƙa´ida sannan ta sanya hannu kan dokokin da suka hana nuna wariya ko bambamci wajen tallafawa mabuƙata.”

An dai ɗauki ƙungiyar a cikin haɗaɗɗiyar ƙungiyoyin agaji masu zaman kansu wato VENRO a matsayin wata ƙungiyar agaji amma ba wata ƙungiyar addinin musulunci ba. Wannan wakilcin da aka ba ta ya sa yanzu ƙungiyar ta VENRO mai wakilai ƙungiyoyi 110 ta ƙara zama cikakka tare da samun wata sabuwar suffa. Wannan dai alama ce dake nuni da cewa yanzu a ɓangaren ba da taimakon jin ƙai da na raya ƙasa a nan Jamus ana bawa ƙungiyoyin musulmi wakilci daidai wa daida da sauran ƙungiyoyi, inji Peter Runge shugaban VENRO sannan sai ya ƙara da cewa.

“Ina iya cewa dai yanzu ƙungiyar Islamic Relief ta zama wani ɓangare na wannan iyali. Hakan kuwa wani gagarumin ci-gaba ne ga wata ƙungiyar agaji.”

Shi ma Tarek Abdel-Alem na ƙungiyar Islamic Relief ya bayyana wannan ci-gaban da cewa ya samar da wani sabon yanayin hadin kai a nahiyar Turai, domin kamar bala´o´i daga Indallahi da matsaloli ba su san wani bambamci ba saboda haka ya zama dole duk wani mataki na taimakon jin ƙai ya samu wani ruhi na haɗin kai.

“Muhimmin saƙon da za mu iya bawa masu tallafa mana shi ne dukkan mu bori ɗaya mukewa tsafi wato aiki iri ɗaya muke yi na taimakawa jama´a ko musulmi ko ba musulmi ba. Akwai ƙungiyoyin kirista da na musulmi da waɗanda ba ruwansu da addini. Dukkan mu a nan Turai muke kuma muna aiki ne kamar yadda dokoki da kuma al´adun Turai suka tanadar."