Ƙungiyar ƙwallon Jamus ta dawo gida | Labarai | DW | 12.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyar ƙwallon Jamus ta dawo gida

Ƙungiyar ƙwallon Jamus ta dawo gida daga Afirka ta Kudu , ta samu tarbe na karamci game da rawar da ta taka

default

Shugaban Jamus zai karrama ´yan wasan Mannschaft

Bayan wata guda cur ana fafatawa,a jiya aka zo ƙarshen gasar wasan cin kofin ƙwallon ƙafa ta duniya a ƙasar Afrika ta Kudu. Kamar dai yadda aka riga aka sani, ƙasar Spain ta ɗauki kofin shekara bana, bayan ta lashe Holland da ci ɗaya mai ban haushi.

Ƙungiyar ƙwallon kafar Mannschaft ta Jamus ta zo ta ukku, a yau ta sauka a filin saukar jiragen sama na birnin Frankfurt, inda dubunan ma´abuta ƙwallo suka yi mata tarbe na karamci.

Duk da cewar ba ta sami nasara ɗaukar kofi ba, Mannschaft ta cencenci a yaba mata, inji shugaban ƙasar Jamus, Christian Wullf,wanda har ma ya yanke shawara miƙa lambar yabo ta mussamman ga ´yan wasan da kuma mai koyar da su Joachim Löw, ya kuma bada dalili da cewa Joachim Löw ya yiwa Jamus komai, saboda haka wajibi ne mu ƙara masa ƙarfin gwiwa ta hanyar liƙa masa lambar yabo.Mun yi farin cikin da aikinsa matuƙa.

Yanzu kuma hankula za su fara karkata zuwa shirye-shiryen gasa ta 2014 a ƙasar Brazil.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita: Zainab Mohamed Abubakar