Ƙungiyar ƙasashen yan baruwan mu sun bada goya bayan ga Iran a game da rikicin makaman nuklea | Labarai | DW | 30.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyar ƙasashen yan baruwan mu sun bada goya bayan ga Iran a game da rikicin makaman nuklea

Ministocin harakokin wajen Ƙasashe membobin Ƙungiyar yan baruwan mu, na ci gaba da zaman taro a birnin Putjaraya na ƙasar Malaisia.

Ƙungiyar ta ƙunshi ƙasashe 114, mafi yawan su, masu tasowa, da su ka haɗa da Iran, da Core ta arewa,ƙasashe 2, su ka yi suna, ta fannin adawa da manufofin Amurika.

A cikin sanarwar share fage, da su ka hiddo, ministocin sun hallita yunƙurin Iran, na inganta makashin nuklea, kazalika, sun ce hukumomin Teheran, na bada haɗin kai ga hukumar Majalisar Ɗinkin Dunia ,mai yaƙi da yaɗuwar makaman nuklea.

A ɗaya hannun kuma, kungiyar, ta yi kashedi ga Amurika da sauran abokan ƙawacen ta, a kan batun kai hari ga Iran.

Ƙasashen Jamaique, Singapour da Chili, masu alaƙar ƙut da ƙut da Amurika, sun nuna rashin amincewa da sanarwar farko da ƙasashen su ka hiddo.

Masharahanta a kan harakokin diplomatia, na dangata wannan goyan da Iran ta samu, a matsayin wata gagaramar nasara.