Ƙunar zafi a Turai na hadasa assara rayuka | Siyasa | DW | 19.07.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ƙunar zafi a Turai na hadasa assara rayuka

Ƙasashen turai sun tsunduma cikin matsanacin zafi da zufa.

A wannan wata da mu ke ciki, Ƙasashen turai sun tsinci kansu, cikin wani yanayi na tsananin zafi, wanda ya zuwa ya hallaka, a ƙalla mutane 7, a yankin arewancin Turai.

A mafi yawan ƙasashen yankin ma´auyin zafi ya wuce lamba kokuma degri 30.

A gabanci France wani magimi ɗan shekaru 53, a dunia, ya ɓingire saboda tsananin zufa da gummi da su ka kai masa karro.

Shine cikwan mutum na 9, da su ka rasa rayuka, a ƙasar sanadiyar zafin, a tsukin mako guda.

Shugaban ƙasa Jaques Chirac ya kiri hukumomin kiwon lahia da magaddan gari daban-daban na ƙasar cewar su matsa ƙaimi, wajen kulla da tsohi, wanda su ka fi fuskantar barazanar illolin zafin.

A Holland mutane 2 su ka kwanta dama, a yankin Nimegue da ke gabacin ƙasar, bayan ma´aunin zafi, ya nuna awo 34.

A ƙasar Spain, tsakanin ranar lahadi da laraba da su ka gabata, tsannin zufa ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2.

A jihohin ƙasar da dama, na´urar awan zafi, ta habra, zuwa kussan awo 40, yanayin da al´umomin ƙasar su ka ce bas u sabna gani ba.

Hatta Britania da yanayin zafin ta, ke da sassauci idan a ka kwatanta da sauran ƙasashen turai, a wannan karro, ta tsunduma cikin ƙuna, tun kwana 3 da su ka wuce.

A wurare da dama, gwamnati ta yi tanadin motocin masu zuba tsakuwa, domin magance liƙewar kwalta ga tayoyin ababen shiga, sannan hukumomin zirga zirgar jiragen ƙasa sun bada umurinin taƙaita gudun jirage.

Makarantun pramari da na Secondri, da ma wasu opisoshi na gwamnati, da masu zaman kansu, sun yanke hukuncin dakatar da aiki, bakin tasakiyar rana, don baiwa ma´aikata da ɗallibai, damar samun wuraren sanyaya rayukan su.

A yau, na´urar awan zafi a Charlwood, da ke kudanci London, ta nuna awo 36, wanda shine mafi tsanani, da aka taɓa gani, tun shekara ta 1911, wato shekaru 95 da su ka wuce.

A Belgium, an samu degre 37, wanda shine mizanin mafi ƙuna a ƙasar, a cewar tsoffafi da massana hasashen yanayi .

Hukumomin kiwan lahia, sun tanadi opisisohin agaji na tafi da gidan ka, domin kawo taimakon gagawa ga dukkan mutanen da su ka kasa, jimrewa mumunar zuffar da ake zubawa a ƙasar..

A ko inna cikin nahiyar turai, zafi ya hadasa hauhawar cinakin glas ko ƙanƙara, pankoki da kuma AC.

Wannan raɗɗaɗin zafin, ya sa mazauna France, sun shiga zullumi, irin na shekara ta 2003, inda mutane dubu 15, su ka rasa rayuka a ƙasar, a dalilin ƙunar rana.

A baki ɗaya, zafin na shekara ta 2003 ya jawo mutuwar mutane dubu 30 a nahiyar turai, mussaman daga ɓangaren tsoffafi.

A ƙasar France ana sa ran, daga ranar alhamis mai zuwa, a ɗan samu rangwame , to amma a ƙasar kamar Jamus massana hasashen yanayi, sun ce alhamis ma´aunin zafi zai nuna digre 38, wanda shine zafi mafi tsanani a tsawan shekaru 100 da su ka wuce a cikin wannan ƙasa.

 • Kwanan wata 19.07.2006
 • Mawallafi Yahouza S.Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btz1
 • Kwanan wata 19.07.2006
 • Mawallafi Yahouza S.Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btz1