Ƙudirin Ministocin kuɗi na duniya a taron IMF | Labarai | DW | 25.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙudirin Ministocin kuɗi na duniya a taron IMF

Ministocin kudi na duniya sun yi alkawarin rage gibin kasafin kudi.

default

Shugaban Asusun bada lamuni na duniya IMF Dominique Strauss-Kahn, daga hagu, da kuma Youssef Boutros-Ghali, shugaban kwamitin harkokin kudi na IMF

Ministocin kuɗi na ƙasashen duniya sun yi alƙawarin rage giɓin kasafin kuɗi na ƙasashensu bisa laákari da matsalar ɗumbin bashi da ƙasar Girka ta tsunduma a ciki. Ministocin sun ci alwashin yin aiki tuƙuru wajen samun daidaito a yunƙurin ƙasashen duniya na farfaɗowa daga badaƙalar tattalin arziki da aka shiga. Ministocin sun yi waɗannan alƙawura ne a ƙarshen babban taron Asusun bada lamuni na duniya IMF da ya gudana jiya a birnin Washington. Ko da yake an sami saɓanin raáyi tsakanin ƙasashe masu cigaban masanaántu da ƙasashe masu tasowa a game da barazanar da ka iya tasowa dangane da matakan farfaɗo da tattalin arzikin, a ƙarshe ministocin sun amince da yin bakin ƙoƙari wajen samar da cigaban tattalin arzikin duniya. Shugaban Asusun bada lamunin na IMF Dominique Strauss-Khan ya buƙaci gwamnatoci su tabbatar da ƙarin haɗin kai a yayin da aka shiga matakin sake bunƙasa bayan matsanancin koma bayan tattalin arzikin da aka shiga a shekarar bara. A jawabin bayan taron Ministocin sun jaddada ƙudirinsu na tabbatar da ɗorewar harkokin hada hadar kuɗaɗe da kuma shawo kan matsalar bashi a tsakanin ƙasashen. A saboda haka suka buƙaci samar da wata manufa da zata dace da muradun ƙasashen don samun daidaito da ɗorewar tattalin arzikin duniya.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

  Edita      : Mohammed Nasir Awal