Ƙokarin samarda zaman lafiya a Pakistan | Siyasa | DW | 21.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ƙokarin samarda zaman lafiya a Pakistan

A yau ne ake kaddamar da tattaunawa tsakanin Tarayyar turai da Pakistan

default

Shugaba Asif Ali Zardari

Za a iya cewar babu wata dangantakar kusantaka tsakanin ƙungiyar Tarayyar Turai da Pakistan. Kasancewar wannan ƙasa tayi nesa da manufofin Turan. Tana  da tasiri ne saboda makwabtakanta da Indiya da Afghanistan, baya ga matsalolin siyasa data sake tsintar kan a ciki. Akan haka ne  ake saran cewar batutuwan tsaro zasu mamaye zauren taron da zai gudana tsakanin Pakistan ɗin daTarayyar Turai.

A watan Yunin shekarar data gabata ne dai EU ta gayyaci shugaban Pakistan Asif Ali Zardari zuwa birnin Brussels. Ganawar dake zama na farkon irinsa tsakanin ɓangarorin biyu.Gayyatar na ɓangaren kokarin turan na  samar da zaman lafiya a Pakistan.

Ba wai kisan gillar da akayi wa mai dakin shugaban ƙasar kuma tsohuwar Primista, watau  Benazir Bhutto ne ya fara haifar da rigingimun siyasa ba, wannan ƙasa dake yanƙin kudancin Asia ta jima da kasancewa cikin tarihin rikice-rikicen siyasa.

EU Kommissar Jose Manuel Barroso Giorgio Napolitano Europa Strategie 2020

Jose Manuel Barroso

Saɓanin da ke tsakanin Rundunar soji, gwamnatin farar hula da sashin shari'a dai na daɗa tsananta kuma abin razanarwa, kasancewar Pakistan ɗin tana mallakar makaman Nukiliya. Ƙazalika, wata matsalar dake cigaba da ciwa Turai tuwo a ƙwarya iata ce, irin alakar da ke tsakanin ƙungiyoyi masu tsananin kishin Islama dake Afghanistan da Pakistan.

A bara nedai shugaban hukumar gudanarwar Turai Jose Manuel Barroso, ya jinjinawa irin rawa da shugaba Zardari na Pakistan ɗin ke takawa wajen yaƙar 'yan Taliban...

" Muna alfahari da kokarinka na mayar da Pakistan kan tafarkin Demokraɗiyya, kuma kayi dukkan abun da zaka yi na  tabbatar da cewar ƙasar bata kasance cibiyar rigingimu, ko kuma haddasa tarzoma a sauran ɓangarorin Duniya ba".

Benita Ferrero Waldner EU Kommissarin für Außenbeziehungen

Benita Ferrero Waldner

 A wancan ganawar dai EU tayi alkawarin cigaban tallafawa tattali da harkokin siyasar Pakistan ɗin.Sai dai waɗannan alkawuran sun ta'allaka ne akan tsohon kwamishinar kula da harkokin ketare na ƙungiyar Benita Ferrero-Waldner  wadda tace .

" A mamadinsa, muna bukatar Pakistan ta cigaba da yaƙi da ayyukan tarzoma. Kana muna saran cewar , ita kanta zata taka rawa a dukkan ɓangarori tare da  tabbatar da intacciyyar gwamnati, ta haka ne zamu aiki tare da Pakistan wajen inganta harkokin Ilimi. Ya zamanto wajibi Pakistan da kanta ta nuna kwazo, kafin mu  kammu mu san me zamu iya yi".

Watanni tara da suka gabata kenan da yin haka. To ko shin akwai abunda Pakistan din tayi na azo a gani dangane da waɗannan batutuwa? Shada Islam, ƙwararriya ce kan Pakistan, a cibiyar nazarin kimiyyar Siyasa ta Turai dakr birnin Brüssels...

" Ina ganin suna da manufar tabbatar da ingantacciyar gwamnati a zukatansu. Babban batu  a Pakistan shine, tsakanin Rundunar ƙasar da farar hula ko waye zaifi samun nasara akan ɗayan, kuma ina tsoro a yanzu haka , domin bisa dukkan alamu Sojoji na shirin sake mamaye harkokin ƙasar. Ilimi dai batu ne da za'a tafiyar dashi a hankali. A yammaci dai, makarantun Allo na haifar da matsaloli, amma wannan muhimmin tsari ne da ba za'a iya kawar a sawwake ba. Da farko dai, ya zamanto wajibi a samarda ingantattun makarantun gwamnati ,wanda  ta haka ne iyaye zasu kauracewa tura 'ya'yansu zuwa makarantun zaure. Kana yaƙi da tarzoma hakki ne na al'umma. Akidar tsanannin kishin addini, yaƙin sunkuru, da tashe-tashen hankula,batutuwa ne da zasu ɗauki lokaci kafin a shawo kansu a pakistan".

Shada na ganin cewar wannan ganawa tsakanin Turai da pakistan dai zai dan yi tasiri, kasancewa  ganawar ta su kadai ba abu ne dake da muhimmanci.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Edita: Umaru Aliyu