ƙoƙarin warware rikicin siyasar Nukiliyar ƙasar Iran | Siyasa | DW | 22.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

ƙoƙarin warware rikicin siyasar Nukiliyar ƙasar Iran

Taron ministocin harkokin waje masu zaunanniyar kujera a Komitin Sulhu da Jamus a Berlin

default

Ministocin harkokin wajen Eu dana ƙungiyyar Nato

Ƙasashen biyar da suka haɗa da Biritaniya da Russia da Faransa da Amirka da ƙasar Sin, na gudanar da taron ne, bisa gayyatar ministan harkokin wajen Jamus, Mr Frank Walter Steinmeir. Ministocin a cewar rahotanni, zasu ƙalailaice halin da ake ciki ne game da rikicin Nukiliyar ƙasar Iran. Ana kyautata zaton cewa taron, zai mayar da hankali ne kan duba wasu ƙarin takunkumi na ladaftarwa da za´a ƙara laftawa ƙasar ta Iran, dangane da shakulatin ɓangaro da take na kin kawo ƙarshen aniyarta na mallakar makamin Atom. To sai dai a yayin da ministocin ke ci gaba da tattauna yiwuwar ƙara ɗaukar matakan na ladaftarwa, hukumomin leken asiri na Amirka a can baya sun shaidar da cewa, Iran ta daɗe da kawo ƙarshen shirinta na ci gaba da sarrafa sanadarin Uranium. Wannan bayani ya haifar da kace-nace a tsakanin da yawa daga cikin ƙasashen Duniya, wanda hakan ne ma ya haifar shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel tayi kashedin cewar: ´´ Merkel ta ce ya zuwa yanzu babu alamar cimma matsaya guda game da kawo ƙarshen wannan rikici, domin Iran ta dage akan aniyarta, idan kuwa haka ne to babu shakka muna nan akan matakan da muke ganin zasu haifar da ɗa mai idanu´´ Rahotanni dai sun nunar da cewa duk da ƙoƙarin da hukumar kula da makamashin Nukiliya ta Duniya, wato IAEA keyi, har yanzu an gaza samo bakin zaren warware rikicin Nukiliyar ta Iran. Iran ba sau ɗaya ba sau biyu ba, ta sha faɗin cewa shirinta na inganta hasken wutar lantarki ne, amma ba na tashin zaune tsaye ba. Duk da irin waɗannan furuce-furuce na Iran, har yanzu ƙasashen yamma na´a mataki ne na rashin gamsuwa da bayanan na Iran, kamar yadda Mr Eckart Von klaeden daga jam´iyyar CDU a nan Jamus ya nunar: ´´ Mr. Von klaeden ya ce abubuwa uku sune suke ci gaba da ɗaukar hankalinmu. Na farko akwai zargin cewa shin aniyar Iran na kera makamin Atom ne ko kuwa na inganta rayuwar ´yan ƙasar. Akwai kuma batu na yadda ƙasar ke goyawa masu tsattsauran ra´ayi baya, a ɗaya hannun kuma ga kallo da ake mata na babbar barazana ga Duniya baki daya´´ A yanzu haka dai akwai rarrabuwar kawuna a tsakanin mambobin ƙasashen dake kwamitin sulhun na Majalisar Ɗin kin Duniya, a game da rikicin Nukiliyar ta Iran. A misali Amirka tuni ta kira Iran a matsayin ɗaya daga cikin shaiɗanun ƙasashe, wanda a ganinta kamata ya yi a saƙala mata tsauraran matakai na ladaftarwa. To amma a waje ɗaya ƙasashe irinsu Russia da Sin nada ra´ayi ne na bin matakan diplomasiyya, wajen warware wannan rikici. Bugu da ƙari ita kanta dangantakar dake akwai a tsakanin Jamus da ƙasar Sin ta ja baya, sakamakon maraba da shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi da shugaban addinin nan na yankin Tibet, wato Dalai Lama a birnin Berlin a watan Satumbar Bara. Bayanai ya zuwa yanzu sun nunar da cewa da alama takun saƙar a tsakanin Jamus da ƙasar Sin ya lafa ƙwarai matuƙa, wanda hakan ne ma ya haifar kakakin ma´aikatar harkokin wajen ƙasar ta Sin, wato Martins Hunters ya tabbatar da cewar: ´´ A yanzu ina ganin takun saƙa a tsakaninmu ya ƙare, komai yanzu ya dawo dai-dai dangane da dangantakar dake tsakaninmu´´ Kafin dai fara wannan taro, Jamus ta buƙaci ƙasashen biyar dasu yi ƙoƙarin cimma matsaya guda, dangane da kawo ƙarshen rikicin Nukiliyar ta Iran, dake ci gaba da ɗaukar hankalin Duniya. Kafafen yaɗa labarai dai sun rawaito ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmier, na cike da fatan cewa taron a wannan karo, zai samu cimma burin da ake buƙata.