1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙoƙarin sasanta rikicin ƙasar Kongo

An ɗage taron sulhu da aka shirya gudanarwa, a tsakanin Gwamnatin Kongo da wakilan ´yan tawaye. Ma´aikatar cikin gida ta ƙasar ta ce za a gudanar da taron ne, a ranar 6 ga watan Janairun sabuwar shekara. Taron zai mayar da hankali ne wajen kawo ƙarshen rikicin dake wanzuwa ne a gabashin ƙasar.Ci gaba da faruwar tashe-tashen hankula a gabashin ƙasar, a yanzu haka ya haifar da hijirar ɗaruruwan mazauna wannan yanki. Ana sa ran wannan taro na gaba, zai samu halartar shugaban ƙungiyyar ´yan tawayen Janar Laurent Nkunda.