Ƙoƙarin Jamus na raya ƙasashe. | Siyasa | DW | 28.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ƙoƙarin Jamus na raya ƙasashe.

Ƙungiyar Haɗin-gwiwar Tattalin arziƙi da Samar da Ci-gaba(OECD) ta yaba wa Jamus bisa rawar gani da take takawa wajen raya ƙasashe.

default

Alamar ƙungiyar OECD

A cikin rahoton da ta fitar a birnin Berlin a jiya Alhamis, Ƙungiyar Haɗin-gwiwar Tattalin arziki da Samar da Ci -gaba, OECD ta yaba wa ƙasar Jamus da taka rawar gani a yaƙin da ake yi da matsalar ɗimamar yanayi da ke addabar duniya, inda a ɗayan hannun kuma ta yi mata suka game da giɓin da take ci gaba da samu na jimilar kuɗaɗen take samu a shekara.

Dala miliyan dubu 12 da ya yi kashi guda bisa goma na kuɗaɗen raya ƙasashe ne dai Jamus ke bayarwa a matsayin gudunmuwarta ga shirin raya ƙasashe a faɗin duniya, inda hakan ya sanya ta a matsayi na uku daga cikin ƙasashen da ke ba da wannan gudunmuwa. Amma kuma duk da haka tana buƙatar ninka kasafinta domin cimma matsayi na kashi 0.7 daga cikin ɗari kafin shekarar 2015.

Hans-Jürgen Beerfeltz

Hans-Juergen Beerfeltz

Hans Juergen Beerfeltz, sakatare a ma'aikatar raya ƙasashe ya kira rahoton na ƙungiyar OECD tamkar ƙwarin-gwiwa ga gwamnatin gamin gambizar CDU/CSU da FDP da ke mulkin Jamus inda yake cewa:

"Mu a matsayinmu na kasar Jamus, ana yaba mana bisa kyakyawar rawar da muke takawa a harkokin ƙasa da ƙasa, musamman ma a fannin kare kewayen ɗan Adam inda muke aikin kare mahalli a faɗin duniya, muke kuma yaƙi da yunwa da talauci."

Shugaban komitin raya ƙasashe na ƙungiyar OECD, Eckhard Deutscher ya jinjina wa Jamus da cewa kamata ya yi ta zamo abar koyi ga sauran ƙasashe, a fannin ba da taimakon raya ƙasashe. Ya ƙara da cewa zai kuma dace a kafa wata ma'aikata ta musamman da za ta rinƙa kula da wannan buƙata saboda cewa za ta iya samun ikon faɗa a ji a majalisar ministoci. Deutscher ya kuma nuna gamusuwarsa game da matakin Jamus na rage abokan aikinta na haɗin-gwiwa daga 84 zuwa 57 cikin shekaru huɗu da suka gabata, sakamakon wani sauyin manufa da Heidemarie Wieczorek-Zeul wadda ministace daga ɓangaren jam'iyar SPD ta jagoranta. Ko shakka babu wannan mataki ya ƙarfafa aikin raya ƙasashe da Jamus ke yi. To amma Deutscher ya bayyana shakkun cewa Jamus na buƙatar kara kasafin kuɗinta na shekarar 2011 domin ta iya ta cika alƙawarin kuɗin da ta ɗauka...

Ya ce "A matsayin ɓangare na kasafin kuɗin shekarar 2012, kamata yayi a yi wani takamammen shiri da zai fayyace ƙaruwar aikin haɗin-gwiwa da raya ƙasashe da Jamus ke yi a kowace shekara, domin cimma ci-gaba na kashi 0.7 bakwai daga cikn ɗari. Gwamnati na buƙatar kau da duk wani buri ta siyasa wajen ba da goyon baya ga wannan shiri tare da kuma bayyanar da shi a fili."

A cikin jawabinsa sakataren ma'aikatar raya ƙasashe, Beerfeltz bai fito fili yayi magana game da buƙatar ƙara kasafin kuɗin ba.

Ya ce:" Muna farin ciki cewa za a samu ƙarin da ba a taɓa samu a shekara mai zuwa, wanda a bayansa za mu gabatar da wani kasafi na daban fiye da yadda lamarin ya kasance a cikin wasu shirye-shirye. Wannan dai abu ne mai sauƙi."

Ƙungiyar OECD ta nuna wa ma'aikatar raya ƙasahe ta Jamus inda ya kamata ta fi mai da hankali. Deutscher ya ba ma'aikatar shawara da ta ba da ƙarin taimako ga ƙasashe mafi rauni da ke fama da matsanancin talauci.

" Kamata yayi a mai da hankali ga ƙasashe masu rauni da waɗanda ke fama da rikice-rikice da kuma ƙasashen da ke yankin kudu da hamadar Sahara."

Bundesentwicklungsminister Dirk Niebel

Dirk Niebel ministan raya ƙasashe a Jamus

Ra'ayin Deutscher ya zo daidai da na ministan raya ƙasashe, Dirk Niebel wanda ya ce a yanzu gwamnatin Jamus ta fi ba da fifiko ne ga ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya na Millenium da ke nufin ragen talauci da kashi 50 daga cikin ɗari kafin shekarar 2015. Dirk Niebel ya ƙara da cewa:

"Tasirin aikinmu na raya ƙasashe zai ƙaru ne daidai da yadda ƙasashen da muke wannan aiki tare da su, su kuma za su ɗauki alhakin da ya rataya a wuyansu. Babu wata ƙasa da za ta iya samun ci-gaba in ba ta samu shugabanci na gari, ta kuma yi yaƙi da cin hanci da rashawa ba. Saboda haka waɗannan sune sharuɗa da za su zamo mizaninmu nan gaba."

Mawallafi: Marcel Fuerstenau/ Halima Balaraba Abbas

Edita: Muhammad Nasiru Awal