Ƙidayar ′yan Luwaɗi a Ƙasar Kenya | Zamantakewa | DW | 12.11.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Ƙidayar 'yan Luwaɗi a Ƙasar Kenya

A ƙoƙarinta na daƙile cutar AIDS gwamnatin Kenya ta tsayar da shawarar ƙidayar 'yan luwaɗi domin tantance yawan masu ɗauke da ƙwayar cutar tsakaninsu

default

'Zanga-zangar 'yan luwaɗi da maɗigo a Johannesburg ta Afirka ta Kudu

A ƙasar Kenya dai an haramta namiji ya nemi ɗan-uwansa namiji, kuma duk wanda aka same shi da wannan laifi, ba da wata-wata ba za a tasa ƙeyarsa zuwa kurkuku. Sai dai kuma a ɗaya hannun ƙasar Kenya na fama da ɗimbim mutane masu ɗauke da ƙwayoyin cutar AIDS abin da ya haɗa da 'yan luwaɗi, a sakamakon haka gwamnati ta fara shawarar gabatar da wani mataki na ƙidaddigar yawan 'yan luwaɗi a ƙasar, lamarin da ba shakka yake da muhimmanci, amma kuma yake tattare da haɗari.

"Sunana Peter, kuma ina alfahari da kasancewa ɗan luwaɗi".

Peter dai ɗaya ne daga cikin 'yan luwaɗi ƙalilan dake bayyana ɗabi'ar halittarsa a fili a ƙasar Kenya ta gabacin Afirka. Doka dai ta haramta wa namiji ya nemi ɗan uwansa namiji a ƙasar ta kuma tanadi hukuncin da ya kai na ɗaurin shekaru 14 a kurkuku akan duk wanda aka same shi da wannan laifi. Amma duk da haka gwamnatin ƙasar ta tsayar da shawarar ƙidayar yawan 'yan luwaɗin tana mai watsi da wannan doka. Fatanta game da haka shi ne ta wannan mataki ta cimma nasarar wayar da kan jama'a akan cutar nan ta AIDS mai karya garkuwar jikin ɗan-Adam in ji Nicholas Muraguri daga hukumar da alhakin lamarin ya rataya wuyanta:

"Mun san cewar gwamnati ta hamarta hakan, amma fa wajibi ne mu gabatarwa da wannan gungu na mutane cikakkun bayanai da kuma tayin da muke ɗauke da shi ta yadda zasu iya kare kansu daga kamuwa da ƙwayoyin cutar."

Kawo yanzun dai babu wasu tabbatattun alƙaluman da aka bayar dangane da ƙasar ta Kenya baki ɗayanta. Amma wani binciken da aka gudanar misalin shekaru biyun da suka wuce ya nuna cewar a yankunan gaɓar tekun ƙasar kusan kashi 50% na 'yan luwaɗi na ɗauke da ƙwayar cutar HIV. Peter Njane, mai fafutukar yaƙi da cutar AIDS ya ce dalilin haka shi ne rashin cikakkiyar masaniya a game da yadda ake kamuwa da ƙwayar cutar:

"Akasarin 'yan luwaɗin na tattare ne da imanin cewar suna da wata kariya a lokacin da suke neman maza. Ba su da wata masaniya a game da amfani da kwaroron roba don kare kansu. A saboda haka nike da imanin cewar wannan ƙidayar zata taimaka wajen magance matsalar."

Sai dai kuma ayar tambaya a nan shi ne, shin 'yan luwaɗin zasu yarda su shiga wannan ƙidaya, sanin cewar doka zata shiga farautarsu. Nicholas Muraguri dai ya san cewar ba za a samu nasara a ƙarkashin wannan sharaɗi ba, amma wataƙila wannan matakin zai haifar da mahawara akan dangantakar luwaɗi da cutar Aids. Akwai buƙatar wayar da kan jama'a cewar bai kamata a mayar da waɗanda Allah Ya jarabce su da wannan ɗabi'a ta neman maza, saniyar ware a al'amuran zamantakewa ba. A wata mai zuwa ne dai gwamnati ke da niyyar fara ƙidayar kuma ga alamu 'yan ƙalilan ne daga cikin 'yan luwaɗin zasu yarda a saka su cikin lissafi.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu