ƙidayar jama´a a tarayya Nigeria | Labarai | DW | 21.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ƙidayar jama´a a tarayya Nigeria

Bayan cece-kucen, da a sha tabkawa, yau ne a tarayya Nigeria, a ka fara ƙidayar jama´a .

Don cimma burin da aka sa gaba a wannan ƙidaya, hukumomi sun ɗauki tsatsauran matakai, na taƙaita kai da kawon jama´a.

Rahotani daga birnin Ikko, sun nunar da cewa, gwamnan jihar, ya umurci al´ummomi million15 na Lagos,da su zauna gidajen su, daga 8 na sahe, har zuwa 6 na yamma, a tsawon kwanki 5.

Wannan mataki, zai shafi sauran jihohin ƙasar a ranekun asabar da lahadi masu zuwa.

A jawabin da yayi ga al´uma, kamin fara ƙidayar, shugaba Olesegun Obasanjo, ya tabbatar da cewa, burin wannan aiki, shine kawai, sannin addadin yawan mutanen Nigeria, saɓanin yadda wasu ke tunanin, za a fake da buzguma ne a harbi karsana.

ƙidayar jama´a ta ƙarshe a tarayya Nigeria, an gudanar da ita, a sherkara ta 1999, a wacen lokaci, yawan jama´ar ya tashi kussan million 89.