Ƙhaddafi, Mubarack da Buteflika sun hadu a birnin Tripolie | Labarai | DW | 24.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙhaddafi, Mubarack da Buteflika sun hadu a birnin Tripolie

A ranar jiya talata, an gudanar da taron ƙoli da ya haɗa shugaban Muhammar Ƙhaddaffi na Libya, da takwarorin sa, Hosni Mubarak na Masar, da kuma Abdel Aziz Buteflika na Algeria.

Shugabanin 3, sun tantanna a kann batutuwa da su ka shafi ƙasashen larabawa, mussamman yankin gabas ta tsakiya, Somalia da Sudan, batutuwan da za su mamaye ajendar taron ƙungiyar gamayar Afrika da za a shirya a mako mai zuwa a ƙasar Ethiopia

Hosni Mubarak, yayi anfani da wannan dama, inda yayi masu bayyanin sakamakon ganawar da yayi da sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice, a makon da ya gabata.