Ƙasashen yamma sun nuna adawa da gudanar sabbin sabbin shawarwari kan Kosovo | Labarai | DW | 13.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙasashen yamma sun nuna adawa da gudanar sabbin sabbin shawarwari kan Kosovo

Ƙasashen yamma a kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya sun nuna adawa da wani shirin Rasha na gudanar da sabbin shawarwari dangane da makomar lardin Kosovo dake cikin tarayyar Sabiya. Jakadan Amirka a MDD Zalmaya Khalilzad ya ce an kai maƙura a shirin tattaunawar bayan wani yunƙuri da aka shafe shekaru biyu ana yi ya kasa samar da wata yarjejeniya tsakanin kabilun Albaniyawan Kosovo da gwamnatin Sabiya. Ɗaukacin ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai da Amirka da ƙasashen musulmi sun nunar da cewa ya kamata a bawa lardin wanda ya balle ´yancin kai bayan rugujewar tattaunawar. To sai dai Sabiya da babbar kawarta Rasha na adawa da wannan shawara. A ranar 19 ga watannan na desamba kwamitin sulhu zai tabka muhawwara akan lardin na Kosovo.