Ƙasashen Turai da kokarin dakile Baƙin haure | Siyasa | DW | 05.06.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ƙasashen Turai da kokarin dakile Baƙin haure

Dubban baƙin haure ne ke cigaba da bin ɓarauniyar hanyar cikin ruwa a hankoronsu na zuwa turai

default

Hanyar shigowa turai ta ruwa

Ga mafi yawan al'ummomin nahiyar Afirka da na yankin gabashin turai dai, Nahiyar Turai na zama wata aljannar Duniya ce. Adangane da haka ne ƙasashen Turan ke bukatar ɗaukar matakan gaggawa dangane da shawo kan matsalar kwararan baƙi daga kasashen ketare.

Anan Tarayyar Jamus dai an fara dasa ayar tambaya dangane da wuyan wannan matakai. Ga 'yan gudun hirar dake bin cikin Tekun Baharun domin ketarewa zuwa turai dai, tamkar tsira ce daga talauci da rigingimun yake-yake.

Sai dai mafi yawan 'yan gudun hijra, kan sadakar da rayukansu ga haɗari, akokarinsu na ganin cewar sun isa nahiyar turai domin inganta rayuwarsu. Kawo wqannan lokaci dai ƙungiyar Tarayyar Turai ta sha kokarin shawo kan wannan matsala ta kwararan bakin haure ,ba tare da samun nasara ba.

Flüchtlinge aus Libyen

Baƙin haure daga Libya

Adangane da hakane a bayyana take cewar, ya zamanto wajibi ƙasashen turan su samarda dokokin da zasu iya saukakawa baƙi damar samun izinin shigowa cikin ƙasashen nasu bisa ka'ida.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗunkin duniya dai ta kiyasata cewar a shekara ta 2008 kaɗai, kimanin 'yan baƙin haure daga Afirka dubu 37 ne suka keta zuwa nahiyar turai ta Tekun Italiya. Kuma bisa dukkan alamu za a samu fiye da wannan adadi a wannan shekara. Kokarin ƙasashen turan a yanzu haka dai shine ganin cewar sun cimma dakatar da dubban 'yan gudun hijira dake kwararowa zuwa nahiyar ta ɓarauniyar hanyar cikin tekun Baharun.

A cewar karamin sakataren dake ma'aikatar harkokin cikin gida dake nan tarayyar jamus Peter Altmaier, hakan na nufin magance matsalar da bakin haure ke fuskanta daga tushe....

"Bawai tsauraran matakai yakamata mu ɗauka ba wajen shawo kan matsalar kwararan baƙin haure, amma taimaka musu daga ƙasashensu na asali, shine ke da muhimmanci. Abunda muke so mu cimma shine karfafa haɗin kai da ƙasashen dake yankin Afirka ta arewa, domin dakile kwararan baƙin haure zuwa turai"

Bürgerkrieg Sri Lanka Flüchtlinge

Sansanin 'yan gudun hijira

A nata ɓangare Lale Akguen na jammi'yyar SPD cewa tayi "dole ne akara zuba jari a fannin taimakon raya ƙasa wa ƙasashe masu tasowa. In dai har ƙungiyar Eu tana muradin rage baƙin haure ya zamanto wajibi ta inganta matsayin rayuwa a kasashen da su bakin suke kaura. Adangane da baki dake takardar shaidar zaman kasa, ya kamata a inganta takardun shaidar zaman ƙasa da suke dashi na dindindin, musamman a ɓangaren kwararrun ma'aikata. Kazalika akwai bukatar daidaita batun bakin da kan zo turai su dade kafin su koma ƙasashensu na asali"

Baƙin Haure da taimakon raya ƙasashe masu tasowa dai, batutuwa ne da ke tafiya kafaɗa da kafaɗa na dogon lokaci, saboda haka ya kamata ayi la'akari da halin da ƙasashensu na asali ke ciki .

Mawallafiya: Zainab Mohammed

Edita: Mohammad Nasir Awal