Ƙasashen Faransa da Jamus sun jadada aniyarsu na taimakawa Gerka | Labarai | DW | 25.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙasashen Faransa da Jamus sun jadada aniyarsu na taimakawa Gerka

Shugabannin ƙasashen Faransa da Jamus sun ce sun samar da hanyoyin cetoƙasar Gerka

default

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Shugaban ƙasar Faransa Nikola Sarkozy

 Shugabanin ƙasashen Faransa da Jamus sun ce sun samar da hanyoyin taimakawa ƙasar Girka da ke fama da matsalar tatalin arziki,shugabannin wanda suka bayyana haka  a birnin Brussel inda ake gudanar da taron ƙungiyar Eu sun ce za a yi amfanin da taimakon hukumar bada lamani ta duniya domin fitar da kasar Girka daga halin ƙaƙa nika yi. ƙasashe da dama na ƙungiyar tun da farko  kamar su  Faransa basu amince ba ba a nemi agaji mayan bankunan na duniya domin magance matsalar ta ƙasar  ta Girka suna masu cewa wannan  wani abu ne da ke  iya nuna kasawar ƙungiyar ta EU wajen magance matsalolinta.Ana san ran a karshen taron da za a yi kwanaki biyu ana yi   shugabanin ƙasashen na ƙungiyar ta EU zasu cimma dadaituwar baki da hukumomin na hukumar lamani ta duniya akan wani shirin taimakawa ƙasar girka da ƙuɗaɗen da zasu iya kai million 20 zuwa 30 na ƙudin Euro.

Mawallafi : Abourahamane Hassane Edita: Tijani Lawal