Ƙasashen duniya sun fara mai da martani game da hukuncin da aka yanke wa Saddam Hussein. | Labarai | DW | 05.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙasashen duniya sun fara mai da martani game da hukuncin da aka yanke wa Saddam Hussein.

Dab da yanke wa Saddan Hussein da muƙarrabansa hukuncin kisa a birnin Bagadaza ne, shugabannin gwamnatoci da manyan jami’an ƙasashe da dama suka fara mai da martaninsu ga hukuncin. Da farko dai Firamiyan Iraqin, Nuri al-Maliki, ya yi kira ga ’yan ƙasarsa ne da ka da su yi wani tashin hankali bayan yanke wa tsohon shugabansu hukuncin kisan. Amma ya kuma yabi hukuncin da cewa, an nuna adalci, ba a kan shi Saddam ɗin kawaia ba, har ma da kan baƙin zamani na duk tsawon mulkinsa.

A birnin Teheran kuma, rahotanni sun ce, jami’an ƙasar sun yabi hukuncin da aka yanke wa tsohon shugaban ƙasar Iraqin. Kazen Jalai, kakakin kwamitin majalisar ƙasar Iran kan batutuwan tsaron ƙasa da harkokin ƙetare, ya ce ya gamsu ƙwarai da hukuncin, saboda Saddam wani riƙaƙƙen mai aikata laifuffuka ne kuma wanda tarihi ma ke sane da shi, saboda yawan zub da jinin bil’Adama da ya yi. Amma wani masharhancin ƙasar Iran ɗin kan harkokin siyasa, Morad Enadi, ya ce yana jiɓinta wannan hukuncin ne da manufofin siyasar birnin Washington da kuma zaɓen Majalisar dattijan ƙasar da za a gudanar gobe.

A birnin Paris, ministan harkokin wajen Faransa, Phillipe Douste-Blazy, ya yi fatar cewa, wannan hukuncin ba zai ƙara janyo taɓarɓarewar al’amura da yaƙe-yaƙe tsakanin mabiya ɗariƙun ƙasar ba.

A Birtaniya kuma, sakatariyar harkokin wajen ƙasar, Margaret Beckett, ta ce tana marhabin labarin cewa Saddam Hussein da muƙarrabansa sun husikanci shari’a, kuma za su huskanci sakamakon laifuffukan da suka aikata. Sai dai ƙungiyar nan mai fafutukar kare hakkin ɗan Adam, wato Amnesty International, ta ce ba a nuna adalci ba wajen a shari’ar da aka yi wa Sadddam Hussein.