Ƙasashen ƙetare na ta ci gaba da hidimar kwashe ’yan ƙasarsu daga Lebanon. | Labarai | DW | 20.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙasashen ƙetare na ta ci gaba da hidimar kwashe ’yan ƙasarsu daga Lebanon.

Kusan ’yan ƙasashen ƙetare dubu 57 ne ke jiran kwashe su da za a yi daga ƙasar Lebanon zuwa ƙasashen Cyprus da Turkiyya ko kuma Siriya. A halin yanzu dai, galibin ƙasashen yamma na kwashe ’yan ƙasarsu ne da jiragen ruwa zuwa Cyprus da Turkiyya. Wasu kuma na jigilar nasu ɗin ne cikin manyan bas-bas zuwa birnin Damascus a ƙasar Siriya, inda daga nan kuma jiragen sama ke kwasansu zuwa ƙasashensu. Ƙasashe da dama dai na kyautata zaton cewa, za su gama kwashe nasu daga Lebanon ɗin kafin gobe juma’a.

A nan gida Jamus kuma, gwamnatin tarayya ta tura jiragen rundunar mayaƙan samanta guda uku zuwa birnin Damascus yau, don su kwaso Jamusawa kusan ɗari 5 da suka tsere daga hare-haren da Isra’ila ke kai wa Lebanon.