Ƙasar Sin ta yi watsi da zargin da Amirka ke yi mata na kasancewa barazana a husakr soji. | Labarai | DW | 25.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙasar Sin ta yi watsi da zargin da Amirka ke yi mata na kasancewa barazana a husakr soji.

Gwamnatin Sin ta yi yi watsi da sukar da Amirka ke yi mata, ta cewa, ta zamo barazana ga duniya a huskar soji. Bugu da ƙari kuma, ta kare kasafin kuɗin da take kashewa kan tsaro da harkokin rundunar sojin ƙasar. Da yake bayyana matsayin mahukuntan birnin Beijin a kan rahoton da ma’aikatar tsaron Amirka, wato Pentagon ta buga, wani kakakin gwamnatin Sin ɗin, ya ce rahoton na ƙara gishiri kan ainihin ƙarfin rundunar sojin ƙasar da kuma kuɗaɗen da mahukuntanta ke kashewa a huskar soji. Duk hasashen Amirkan na dogaro ne kan irin tunanin da ake yi a lokacin yaƙin cacar baka, inji kakakin.

A ran talatar da ta wuce ne dai, ma’aikatar tsaron ta Pentagon da ke birnin Washington, ta buga rahoton, inda ta ce matakan bunƙasa da kuma inganta rundunar sojinta da Sin ke yi, ya sa ta kai matsayin duk wata ƙasa a duniya, wadda za ta iya shiga tserereniya da Amirka a huskar soji. Rahoton ya kuma ƙiyasci cewa, kasafin kuɗin da Sin ta ware wa fannin sojinta takamaimai, ya ninka wanda mahukuntan ƙasar suka bayyana, har sau biyu ko sau uku.