Ƙasar Girka ta wayi gari cikin zanga-zanga | NRS-Import | DW | 05.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Ƙasar Girka ta wayi gari cikin zanga-zanga

A Girƙa an shiga zanga-zangar nuna adawa da shirin tsuƙe bakin aljihu.

default

Tutar 'yan zanga-zanga

A ƙasar Girka, an samu arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zangar nuna adawa da shirin tsuƙe bakin aljihu inda a sakamakon haka aka dakatar da zirga-zargar jiragen sama da na ƙasa da na ruwa. Sai da kuma 'yan sandan suka yi amfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa gungun 'yan zanga-zanga guda hamsin da suka yi yunƙurin yi wa ginin majalisar dokokin ƙasar ƙawanya. Hakazalika a garin Thessaloniki sai da wasu matasa su ka ta jefa duwatsu ga tagogin kantuna ko kafin a tarwatsa su da barkonon tsohuwa. A tsakiyar daren jiya ne kuma aka dakatar da tashin jiragen sama tare da rufe makarantu, ma'aikatun gwamnati da kuma wurare yawon shaƙatawa da suka haɗa da Acropolis. An kuma dakatar da yaɗa labarai ta rediyo da telebijan. An shiga wannan zanga-zanagr ne domin nuna adawa da matakan da gwamnati ta ɗauka a ƙarshen mako domin samun rancen biliyoyin euro daga asusun ba da lamuni na duniya.

Mawallafiya: Halima Abbas

Edita: Umaru Aliyu