Ƙasar Brundi ta dakatar da aiki wakilin ƙungiyar kare hakin bil adama na Human Rights Watch | Labarai | DW | 19.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙasar Brundi ta dakatar da aiki wakilin ƙungiyar kare hakin bil adama na Human Rights Watch

Gwamnatin ƙasar Burindi ta ummarci Wakilin ƙungiyar Human Rights Watch da ya fice daga ƙasar

default

Tutar ƙasar Burindi

Gwamnatin ƙasar Burindi ta bada ummarnin kora'r wakilin ƙungiyar kare hakin bil adama na Human Rights watch daga birnin Bujumbura, kafin nan da ranar biyar ga sabon wata mai shiri kamawa,bayan dakuma ta dakatar da aikinsa tun a ranar 18 ga wannan wata.

A cikin wata wassiƙa  da ministan  kula da harakokin waje na ƙasar ta Brundi ya aike da ita ga Mista Neela Ghoshal, ya gargaɗeshi da ya tatara irin na sa ya fice daga ƙasar, saboda abinda gwanatin ta kira katsa lodon a cikin harakokin cikin_gida da mista Neelan ya ke yi masu .

Mista  Neelan dan asilin ƙasar Amurka wanda ke zaune a ƙasar ta Brundi, tsawon shekaru ukku, ya sha rubuta bahasin da ƙungiyar kare a hakin bil adaman ta human Right wacht ke baiyyanawa akan cin zarafin jamaa dakuma take hakin bil adama,a ƙasar ta Brundi, a dadai lokacin da ake shirin fara zaɓen ƙananan hukumomi a ranar jumaa mai zuwa.

Mawallafi Abdourahamane Hassane

Edita Ahamad Tijani Lawal