Ƙarshenn ziyara Ronald Yamamoto a Tchad | Labarai | DW | 25.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙarshenn ziyara Ronald Yamamoto a Tchad

Matamakin sakataran harakokin wajen Amurika mai kula da nahiyar Afrika, Donald Yamamoto,, ya gaskanta zargin da shugaba Idriss Deby yayi wa hukumomin Sudan, na rura rikicin tawaye a Tchad.

Bayan ya gana da shugaban ƙasar Tchad, Yamamoto ya kiri taron manema labarai, inda ya bayana ƙarara cewar, Tchad haƙiƙa, na fuskantar barazana daga Sudan.

Ya kuma tabatar da gwamnatin Amurika na bada goya baya 100 bisa 100 ga al´ummomi da hukumominTchad, ta fannin yaƙar yan tawaye.

Sannan, ya gayyaci yan siyasar ƙasar, da su haɗa kai, su fuskanci ƙalu-balen rikicin tawaye , a maimakon su ci gaba da zargin juna.

Yau ne Donald yamamoto ke kammala wannan ziyara ta yini 2.

Ya kuma yi anfani da wannan dama, inda yayi masanyar ra´ayoyi, da hukumominTchad, a game da tantanawar da a ke, tsakanin tawagar Tchad da ta bankin Dunia, a game da rikicin kuɗaɗen Man Petur, mallakar gwamnatinTchad da Bankin Dunia ta saka wa takunkumi.