Ƙarshen zanga Zanga a Nepal | Labarai | DW | 25.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙarshen zanga Zanga a Nepal

Jamíyun yan adawa a ƙasar Nepal sun janye zanga zangar gama gari da suka ƙaddamar ta tsawon makwanni biyu, bayan da basaraken ƙasar, Sarki Gyanendra ya amsa buƙatun su na maido da tsohguwar majalisar dokokin ƙasar da ya rushe a bara. A waje guda kuma yan tawayen Maoist waɗanda suka mara baya a ɗaukacin kwanakin da aka yi ana zanga zangar, sun yi fatali da buƙatun da sarkin ya gabatar, abin da ke nuni da cewa har yanzu tsugune ba ta ƙare ba. Jawabin sarki Gyanendra, na tabbatar da mika ragamar mulki ga hannun zaɓaɓɓun wakilan alúma ya sami karɓuwa ga jamaá waɗanda suka yi dandazo a babban birnin ƙasar Katmandu cikin murna da annashuwa ta nasarar da suka samu.