Ƙarshen yajin aiki a Faransa | Labarai | DW | 25.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙarshen yajin aiki a Faransa

Bisa dukkan alamu an kawo ƙarshen yajin aiki a cikin matatun man fetir na Faransa

default

Ma'aikata masu yajin aiki sun toshe hanyar shiga wata matatar mai a Faransa

Ma'aikata dake yajin aiki a matatun man fetir na ƙasar Faransa sun kaɗa ƙuri'ar amincewa da katse hamzarin yajin aikin. Wannan mataki dai ya biyo bayan babban taron da 'yan ƙwadogon suka gudanar ne. Da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP, ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyoyin ƙwadogo na CFDT Jean Luc Bildestein ya shaida cewa a makon gobe ne dai dukannin matatun za su fara aiki.

Kimanin dai matatu guda 12 waɗanda ke gabashin ƙasar za su koma bakin aikinsu bayan tsaikon da suka kawo akan sha'anin sufiri saboda ƙarancin man makonin biyu da suka wuce.

Wannan kaɗa ƙuria'a dai ya biyo bayan awowi kaɗan da 'yan majalisar wakilai da kuma dattawa suka amince da wani daftarin da zai kai ga amincewa da dokar a ranar Laraba mai zuwa.

Gwamnatin shugaba Nikolas Sarkozy dai na son kawo gyara ne ga dokar ta fansho domin kiyaye ƙasar ga faɗawa cikin matsalar kasa biyan kuɗaɗen fansho a cikin shekaru na gaba.

Dokar ta tanadi ƙara yawan shekarun ritaya daga shekaru 60 zuwa 62 abin da ƙungiyoyin ƙwadagon ke adawa da shi.

Mawallafi: Abdourrahmane Hassane

Edita: Mohammad Nasiru Awal