Ƙarshen taron wakilan ƙasashe mafi talauci a dunia a birnin Gao | Labarai | DW | 17.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙarshen taron wakilan ƙasashe mafi talauci a dunia a birnin Gao

A lokacin da ƙasashe 8, masu ƙarfin fada aji a dunia, su ke gudanar da taro a birnin Saint Petesbourg, su kuwa ƙasashe mafi talauci a dunia, sun shirya nasu taron, a birnin Gao da ke arewacin ƙasar Mali.

Wakilai a wannan taron matalauta,sun bayana takaici, a kan ɗaukar sakainar kashi, da shugabanin G8, su ka yi wa harakokin tatalin arziki, da inganata rayuwa a ƙasashen Afrika.

Madame Barry Aminata Toure, shugabar hukumar tattalin arzikin ƙasashen Afrika, CAD Mali, ta yi Allah wadai ,da taron G8 wanda bai haifar da komai ba, a cewar ta, na azo agani.

Sannan tace hatta da shawara da magabatan G 8 su ka yanke bara ta yafe bassusukan da su ka tambayo wasu ƙasashen Afrika, bulla ce , domin har yanzu Afrikawa basu gani ba a ƙass.

Taron gao shine karra na 5 da kasashe matalauta su ka shirya.

A wannan karro, sun tantana a kan matsalolin talauci da gudun hijira.

A ɗazunnan nan ne, aka rufe taron bayan mahaurori masu zafi, akan bassusukan Afrika, da batutuwan yancin ɗan Adam da kuma matsalolin ƙarancin abinci.