Ƙarshen taron ministocin mahhalli na ƙasashen G8 | Labarai | DW | 17.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙarshen taron ministocin mahhalli na ƙasashen G8

Ministocin mahhali na ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki, da takwarorin su na Sin, Mexique, India, Brazil, da Afrika ta kudu, sun kamalla zaman taron yini 2 a birnin Postdam da ke kusa da Berlin, a nan ƙasar Jamus.

Ministocin sun yi masanyar ra´yoyin a game ɗumama da kuma gurɓacewar yanayi , matsaloli fda le tatre da iloli maus yawa a rayuwar bani adama, da kuma tsirai da ma dabbobi a wannan dunia.

Ministocin sun yi kira ga ƙasashen masu ci gaban masana´ antu, su ɗauki matakan rage bankaɗa hayaƙin Gaz a sararin samaniya.

Sannan sun yi kira ga ƙasar Amurika ta bada haɗin kai, ga yarjejeniyar Kioto, wadda ta tanadi hanyoyin yaƙi da taɓarɓarewar yanayi.

Ministan kasar Jamus mai kulla da kare mahhali Sigmar Gabriel ya bayyana mattukar gamsuwa a game da sakamakon taron na Postdam:

„Na yi farin ciki matuƙa da kyaukayawan sakamakon da mu ka samu.

Bayan mahaurorin da mu ka tapka, mun cimma matsaya ɗaya a kan wani daftari wanda zai kasance gishinƙin yaƙi da taɓarɓarewar yanayi, yanzu abun da ya rage shine, aiwatar da shi“.