Ƙarshen taron ministocin harakokin wajen G8 a Postdam | Labarai | DW | 31.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙarshen taron ministocin harakokin wajen G8 a Postdam

Ministocin harakokin waje na ƙasashe 8 masu ƙarfin tattalin arziki a dunia sun kamalla taron su, a birnin Postdam na ƙasar Jamus.

Saidai a taron manema labarai na haɗin gwiwa, da su ka shirya, domin bayyana sakamakon taron, an fuskanci ɓaraka, mussamman tsakanin sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice, da takwaranta na ƙasar Russia, Sergeui Lavrov.

Mahimman batutuwan da su ka kasa cimma daidaito kansu, sun haɗa da rikicin gabas ta tsakiya, inda Russie ƙarara ta bayyana adawa da manufofin Amurika a wannan yanki.

Wannan haɗuwa ta Ministocin harakokin wajen G8,na matsayinshare fage ga taron ƙoli na shugabanin ƙasashen 8, da zai gudana mako mai zuwa a an ƙasar Jamus.