Ƙarshen taron Majalisar Ɗinkin Duniya. | Labarai | DW | 04.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙarshen taron Majalisar Ɗinkin Duniya.

Babbar mashawartar majalisar ɗinkin duniya ta kammala zaman taron ta a birnin New York tare da kira ga ƙasashe su ɗau matakan kare sauyin yanayin muhalli da yaƙi da talauci da kuma ayyukan yan tarzoma. Shugaban majalisar Srgjan Karim tsohon Ministan harkokin wajen Macedonia yace shugabanin ƙasashe kimanin ɗari ɗaya ne suka halarci muhawarar majalisar karo na 62. Sassan kwamitocin majalisar za su cigaba da shawarta kwaskwarimar da ake son yiwa majalisar wanda ya haɗa da batun kare haƙƙin ɗan Adam da shirin tallafin raya ƙasa ga ƙasashe masu tasowa. A jawaban su daban daban shugabanin ƙasashen Afrika sun baiyana cewa rashin cika alƙawuran da manyan ƙasashe masu arziki suka yiwa ƙasashe matalauta, na haifar da tsaiko wajen cimma burin rage talauci da samar da kyakyawan yanayin muhalli. Shugaban Nigeria Alhaji Umaru Musa Yar Aduá yace abin da ƙasashen Afrika ke buƙata shine ƙawance na gaskiya da zuba jari domin cigaban tattalin arzikin nahiyar.