Ƙarshen taron AU a Addis Ababa | Labarai | DW | 31.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙarshen taron AU a Addis Ababa

A daren jiya ne shugabanin ƙasashe da na gwamnatocin ƙungiyar tarayya Afrika su ka kammala zaman taron yini 2, a birnin Addis Ababa na ƙasar Ethiopia.

A jawabin sa na rufe taro, saban shugaban ƙungiyar AU John Kufor, ya yi kira ga ƙasashe Afrika su taimaka, domin aika rundunar kwantar da tarzoma a ƙasar Somalia da ke fama da yaƙe -yaƙe.

Ya ce daga jimmilar dakaru dubu 8, da rundunar ke bukata, a halin yanzu, dubu 4 kawai a ka samu.

Ya zuwa yanzu, ƙasashe 5 kurum ,su ka alƙawarta bada gudumuwar sojoji, a cikin wannan runduna.

A ɗaya hannun, ƙungiyar AU, ta bayana samun ci gaba, wajen kawo ƙarshen rikicin yankin Darfur na Sudan, ta hanyar amincewar hukumomin Khartum, na karɓar rundunar shiga tsakanin ta Majalisa Ɗinkin Dunia.

Sakataran Majalisar, Ban ki Moon, da ya halarci taron,shima ya bayana gamsuwa a game da wannan mataki.

Ta fannin ƙarfafa mulkin demokraɗiya a Afrika, ƙungiyar AU ta ƙirƙiro, wani daftari, a sakamakon taro, sannan ta yi kira, ga ƙasashe masu hannu da shuni, su taimakawa Afrika, wajen yaƙi da hamada.