Ƙarshen taron AIDS a Afrika ta Kudu | Labarai | DW | 09.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙarshen taron AIDS a Afrika ta Kudu

Wakilai fiye da dubu 4, daga sassa daban-daban na dunia, sun kammalla zaton taro, a birnin Durban na Afrika ta kudu , inda su ka tabka mahaurori ,a game da cutar Aids.

Mahalarta wannan taro, sun cimma matsayi guda, a game da wajibcin ƙarfafa matakan yaƙi da wannan annoba, da ta zama ruwan dare a nahiyar Afrika.

Al´ammrin ya ta´azara, a ƙasar Afrika ta kudu, inda alƙalluma su ka nunar da cewa, a ko wace rana ɗaruruwan mutane ke rasa rayuka, a sanadiyar Sida, ko kuma cuttutukan da ke tatare da ita.

Mahalarta taron Afrika ta kudu, sun shawarci ƙasashen da ke fama da cutar, su jaraba yin sallatazuwa ko kuma kungullum ga yara , domin bincike ya gano cewar wannan mataki, na da matuƙar tasiri, wajen hana yaɗuwar cutar Aids.

Ƙungiyoyi masu zaman kansu, da su ka halarci taron ,sun nuna rashin gamsuwa, da matakin da ƙasashen G8 su ka ɗauka, a birnin Heiligendamm, na bada taimakon dalla milion dubu 60, ga nahiyar Afrika, domin yaƙi da cutar Sida.