Ƙarshen taron Ƙungiyar ASEM a Hamburg | Labarai | DW | 29.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙarshen taron Ƙungiyar ASEM a Hamburg

Ministocin harakokin waje na ƙasashen ƙungiyar gamayya turai,da takwarorin su na yankin Asia sun kawo karshen zaman taron da su ka fara jiya, a birnin Hamburg da ke arewacin ƙasar Jamus.

A tsawan yini 2, ministocin harakokin waje na ƙasashen fiye da 40, sun tantana a game hanyoyin ƙarfafa mu´amila tsakanin turai da Asia, ta hanyar ƙungiyar haɗin kai ta ASEM.

Saidai wannan taro ya gudana a cikin yanayin zanga-zanga, inda mutane a ƙalla dubu 6 su ka fito atitina domin yin Alah da shi.

Mahimman batutuwan da sanarwar ƙarshen taron ta ƙunsa, sun haɗa da bukatar ƙungiyar ASEM ta yin belin jagoran yan adawar ƙasar Birmania Aung San Suu Kyi.