Ƙarfafa haɗin kan tsaro da al´adu tsakanin Nijeriya da Nijer | Zamantakewa | DW | 11.12.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Ƙarfafa haɗin kan tsaro da al´adu tsakanin Nijeriya da Nijer

Naɗin jakadan Nijer a Nijeriya a matsayin garkuwan wasu jihohin arewa 17

default

Taswirar Nijeriya da babban birnin tarayya Abuja a tsakiya

A ci gaba da ƙoƙarin samo ƙwararan hanyoyin ƙarfafa tsaro da zumunci da kyautata al´adu a tsakanin Janhuriyar Nijer da Tarayyar Nijeriya, Sarkin Sasa Alhaji Haruna Mai Yasin ya naɗa jakadan ƙasar Nijer a Nijeriya Alhaji Ibrahim Musa a matsayin garkuwan masarautun jahohi 17 na gabacin Nijeriya domin ya riƙa haɗa kan sarakuna ƙasashen biyu kan harkokin da suka shafi tsaro da walwalar jama a. Wannan matakin ya samu amincewar ministan tsaro na Nijer. Ana fata wannan sarautar ta garkuwan za ta ƙara zama wata kafar ƙara samun tsaro a tsakanin Nijer da Nijeriya tare da yawaitar arziki da fahimtar juna tsakanin al´umomin ƙasashen biyu.

Sauti da bidiyo akan labarin