Ƙarancin abinci a duniya | Labarai | DW | 16.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙarancin abinci a duniya

Duk da raguwar yawan masu fama da yunwa a duniya har yanzu da sauran jan aiki a gaba

default

Manomin shinkafa a ƙasar Kenya, inda kamar a ƙasashen Afirka da dama ake fama da matsalar ƙarancin abinci

A yau Asabar ne Majalisar Ɗinkin Duniya ke gudanar da bukin ranar abinci ta duniya. Bisa ga wani rahoton da aka gabatar a wani taron ƙoli a birnin Rom na ƙasar Italiya, aƙalla mutane miliyan 925 a duk faɗin duniya ke fama da rashin abinci mai gina jiki, wanda ya nuna cewa alƙalumman sun ragu daga fiye da mutane miliyan dubu ɗaya a shekarar 2009. Majalisar ta ce wannan ci-gaba ne, amma har yanzu akwai sauran aiki, tun da alƙalumman na da yawa sosai. A yayin da Paparoma Benedict na 16 ke jawabin sa na bukin wannan rana, ya yi kira da a haɗa kai wajen shawo kan matsalar yunwa, inda ya ce tana ɗaya daga cikin ƙudurorin ɗan Adam da ke bukatar ɗaukar matakan gaggawa don magance shi, musamman a yanayin da muke ciki. Ƙungiyoyin agaji sun ce ƙarin farashin kayayyaki, canjin yanayi da matsalar filayen noma da ke addabar ƙasashe masu tasowa, su ne manyan matsalolin da ke hana shawo kan matsalar yunwa a duniya.

Mawallafiya: Pinado Abdu

Edita: Mohammad Nasiru Awal