1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ƙara yawan sojoji a Afghanistan

Halin tsaro a Afghanistan ya ƙara taɓarɓarewa inda a cikin shekaru biyu da suka wuce yawan hare hare na makamai ya ninka har sau 300. Wato kenan lokaci yayi na ɗaukar sabbin matakai.

default

Janar Stanley McChrystal

 Akan haka ƙungiyar tsaro ta NATO za ta yi wani babban taro ranar Laraba a birnin London don duba sabbin dubarun tinkarar rikicin na Afghanistan. Wannan shawara ta sauyin dubarun ta fito ne daga babban kwamandan rundunar ISAF Stanley McChrystal, wanda ke da ƙwarewa ta yaƙi da ´yan tawaye a Iraqi. Janar Mc Chrystal ya yi fatan cewa ƙarin yawan dakaru a Afghanistan zai raunana Taliban ta yadda shugabanninta za su amince da wata yarjejeniyar zaman lafiya.

Kamata yayi nasarar da aka samu a Iraqi a samu irinta a Afghanistan, wato sojoji su fatattaki ´yan tawaye daga wani yanki, a tabbatar da tsaron yankin kana a ƙarshe a sake gina wannan yanki. Sai dai kawo yanzu aikin sake gina lardunan ƙasar bai kankama ba domin wurare da sojojin suka kame sun kasa mayar da su ƙarƙashin ikonsu. Shugaban rundunar ƙasa da ƙasa a Afghanistan ISAF, wato Stanley Mc Chrystal yayi kira da a ƙara yawan sojoji dubu 40 don yaƙar Taliban sannan a lokaci guda a inganta hulɗa da fararen hula.

"Abu mafi tasiri kuma mafi muhimmanci na yaƙar abokan gaba shi ne kyautata hulɗa da mutane, sauraron koke-kokensu don a ƙara fahimtar halin da ake ciki domin bawa jama´a kariya. Dole mu inganta ayyukanmu."

Burin farko dai shi ne rundunar ISAF ta tabbatar da tsaro a manyan birane 10 na Afghanistan. Sojoji su sake ƙwace yankunan da aka yi asararsu ga Taliban shekara ɗaya da rabi da ta wuce. Shi ma shugaban Amirka Barack Obama ya goyi da bayan wannan shawara ta McChrystal.

"Na yanke shawara musamman don kare buƙatun ƙasarmu, za a aike da ƙarin sojojin Amirka dubu 30 zuwa Afghanistan."

A cikin watanni ƙalilan masu zuwa Amirka za ta tura ƙarin sojoji dubu 30 maimakon dubu 40 da McChrystal ya nema. McChrystal na mai ra´ayin cewa ƙara yawan dakarun ƙetare shi ne mafi dacewa wajen cimma burin da aka sa gaba na tabbatar da tsaron lafiya da rayukan jama´a a Afghanistan.

"Muna buƙatar ƙarin dakaru da haɗaka da ta dace wato ba sojoji zalla ba, a´a har da ´yan sanda, jami´an leƙen asiri sojoiin Afghanistan da na NATO wadda Jamus ke cikinta."

A babban taron birnin London kan Afghanistan da zai gudana a wannan makon za a tattauna kan gudunmawar da NATO za ta bayar, to sai dai ana gani ita ma gwamnati a birnin Kabul alhaki ya rataya wuyanta na ƙara samar da tsaro kamar yadda aka ji daga bakin ministan cikin gidan Afghanistan Mohammed Hanif Atmar.

"Za mu ƙara yawan ´yan sanda dubu 160 da sojojin Afghanistan dubu 240 don nuna goyon bayanmu ga shawarar baya-bayan nan da Janar McChrystal ya bayar kan sabbin dubarunsa ga Afghanistan."

Ban da yawan sojojin da za a ƙara janar ɗin na Amirka ya yi kira da a inganta tare da ƙarfafa atisaye tsakanin dakarun kiyaye zaman lafiya da na Afghanistan da kuma gudanar da sintiri na bai ɗaya.

Dole a jira har tsakiyar shekara ta 2011 a gani ko wannan ra´ayi na janar ɗin zai haifar da wani abin kirki domin a wannan lokaci ne al´umar Afghanistan za su san cewa ´yan tawaye ba su yi galaba ba.

Mawallafa: Andreas Noll/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Madobi