Ƙabilar Basarwa ta Botswana ta ka da gwamnatin ƙasar a kotu. | Siyasa | DW | 14.12.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ƙabilar Basarwa ta Botswana ta ka da gwamnatin ƙasar a kotu.

A wata shari’ar da aka daɗe ana ta yi, babban kotun ƙasar Botswana, ta yanke hukuncin bai wa ’yan ƙabilar nan ta Basarwa gaskiya, game da ƙarar da suka kai gabanta inda suke ƙalubalantar gwamnatin ƙasar dangane da ta da su daga gandun da suke tun fil azal, a kan dole. Yan ƙabilar dai na neman su koma kan gandun kakanin kakaninsu ne a yankin hamadar Kalahari, inda aka ta da su a kan dole, saboda haƙo ma’adinan lu’u’lu’u a wannan yankin da gwamnatin ƙasar da kamfanonin ƙetare ke niyyar yi.

'Yan ƙabilun Bushmen na Botswana suna ƙayatad da shugabannin ƙetare da ke ziyarar ƙasar.

'Yan ƙabilun Bushmen na Botswana suna ƙayatad da shugabannin ƙetare da ke ziyarar ƙasar.

Shari’ar dai, ita ce mai tsawo a tarihin Botswana. Kafin a yanke hukuncin, masu sa ido da kafofin yaɗa labarai sun yi ta raɗe-radin cewa, watakila alƙalan kotun, za su miƙa wuya ga angizon da gwamnatin ƙasar ke yi musu a bayan fage. Game da hakan ne kuwa, masu ɗaukaka ƙarar, wato ’yan ƙabilar Basarwa, daga al’umman nan da ake kira Bushmen, waɗanda su ne aka sani tamkar ’yan asalin yankin hamadar Kalahari, suka lashi takobin cewa, za su ci gaba da gwagwarmayarsu har zuwa lokacin da su sami nasara, wato ta komawa gandunsu, inda aka ta da su a kan dole zuwa wasu yankuna daban:-

„Za mu ci gaba da wannan fafutukar, har zuwa lokacin da za mu sake mallakar ƙasarmu ta gado, da ke tsakiyar gandun dajin Kalahari. Burin rayuwata, shi ne in sake ’yanto ƙasar kakannin kakannina. An kori al’ummarmu daga ƙasarsu ta gado, ta kakannin kakanninsu. Amma Allah ya ba mu ƙarfi da kuzarin ci gaba da wannan gwagwarmayar, ta ’yanto ƙasarmu, wadda ke ɗauke da sunayenmu. Sabili da haka ne nake ta wannan ƙoƙari don in samar wa al’ummanmu matsugunarsu.“

Roy Sesana ke nan, wani mai faufutukar kare hakkin ɗan Adam na ƙabilar Basarwa. A cikin gandun dajin Kalaharin dai aka haife shi. Kuma nan ya tashi, ya yi tsawon duk rayuwarsa. A halin yanzu dai riƙaƙƙen magorin ’yan wannan ƙabilar ne, inda yake samar musu magungunan gargajiya, idan ba su da lafiya, ko kuma don warkad da cututtukan da suke fama da su. Tun ƙarshen shekarun 1990 ne, shi da wasu ’yan ƙabilar na Basarwa, su ɗari 2 da 48, suka kai ƙarar gwamnatin Botswanan gaban kotu. Kukansu dai shi ne:- Gwamnatin ta yi amfani da ƙarfin jami’an tsaro, wajen ta da su kan dole daga matsugunansu na asali, wato a yankin hamadar Kalahari, inda kakannin kakanninsu suka yi zama tun fil azal, inda kuma aka haife su, su kuma suke ci gaba da zama har ya zuwa yanzu; aka kai su wani gu daban, inda yanayin bai dace da halin rayuwarsu na gargajiya ba. A shekara ta 2002, wata kotun da ke shari’ar ta yi watsi da ƙararrakinsu. Amma ba su saduda ba. Sun ci gaba da ɗukaka kara ne har zuwa wannan lokacin, inda babban kotun ƙasar ta ba su nasara.

Da suke yanke hukuncin, alƙalan kotun guda uku, sun bayyana cewa gwamnatin ba ta bi ƙa’ida ba wajen ta da ’yan ƙabilar Basarwan kan dole, ba tare ma da tattauna batun da su ba, kafin yin hakan. Bugu da ƙari kuma, sun ce gwamnatin ba ta da izinin hana su komawa kan ƙasarsu ta gado.

Al’umman Bushmen ɗin dai gaba ɗaya, sun gamsu ƙwarai da wannan hukuncin, tare da bayyana cewa, a ƙarshe sun sami nasara bayan sun shafe shekaru da dama suna ta gwagwarmaya.

Game da bayanan da gwamnatin ƙasar ta bayar, wai ta ɗau matakin ne don raya duk yankunan karkarar ƙasar, abin da ya ƙunshi gandun dajin Kalaharin ma, inda ’yan ƙabilar Basarwan suke, Roy Sesana ya bayyana cewa:-

„Duk ƙarya suke yi. Da yawa daga cikinmu sun ziyarci makaranta. Amma babu wata moriyar da muke ci daga yin hakan. Ku dubi duk ko’ina a ƙasar nan, nawa ne daga cikin ’yan ƙabilarmu suke aikin kiwon lafiya, nawa ne ke karantarwa ? Wai shin ko za ku iya ba ni sunan mutun ɗaya daga ƙabilarmu, wanda aka ɗauka aiki a hukumomi, ko ma yake cikin gwamnati? Mutanenmu nawa ne ke aiki da Rediyo Botswana, don bayyana tarihinmu? Ko ɗaya babu! A makarantun ƙasar nan, ba a karantad da al’adunmu, ko harshenmu. Duk ababan da suka shafi harkokin rayuwarmu, ba a karantad da su a makarantar. To ta hakan, kuna son in yi ta yabon wannan ƙasar ne?“

Shari’ar dai ta sami sha’awar ɓangarori da dama na cikin gida da kuma ƙetare, saboda tana alamta irin gwagwarmayar da al’ummomi ’yan tsiraru ke yi ne da hukumomi a ƙasashe daban-daban na duniya. Ƙungiyoyin kare hakkin ɗan Adam da dama sun yi ta nuna goyon bayansu ga ƙabilar ta Basarwa a lokacin shari’ar. Kuma a halin yanzu, suna cikin masu taya su murna game da wannan nasarar da suka samu.

 • Kwanan wata 14.12.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btx2
 • Kwanan wata 14.12.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btx2