1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ɓarin wuta tsakanin Isra´ila da Hezbollah

Yahouza S. MadobiJuly 20, 2006

A na ci gaba da lugguden wuta tsakanin dakarun Isra´ila da na Hezbollah

https://p.dw.com/p/Btyy
Hoto: AP

Da sanhin sahiyar yau, an ci gaba da lugguden wuta, ta gaba da gaba, tsakanin dakaraun Isra´ila da na Hezbollah a kudancin Labanon, kussa da yankin da dakarun Hezbollah su ka hallaka sojoji 2, na Isra´ila, a bata kashin da su ka yi jiya.

A yayin da a ka shiga kwana na 9, da fara yaƙin ranar jiya, ta kasance wada a ka fi samun assara rayuka, inda a ƙalla mutane 72 fara hulla su ka rasa rayuka a Labanon, da kuma sojoji 2 a ɓangaren Isra´ila.

Daga daren jiya zuwa sahiyar yau, jiragen yaƙin Isra´ila sun yi amen wuta cikin wani gehen ƙarƙashin ƙasa, inda su ke kauttata zaton, shugabanin Hezbolah sun samu mafaka.

Saidai a sanarwar da su ka hido, yan Hezbollah sun tabatar da cewa, babu shugaba ko ɗaya da ke ciki a lokacin da ka kai harin.

Baki ɗaya mutane kussan 350 su ka rasa rayuka, rabin milion su ka shiga gudun hijira a sakamakon wannan saban yaƙi.

Daga sashen iyaka da Syria, rundunar Isra ´ila ta ƙara ruwan bama bamai, domin hana wucewar makamai zuwa Labanon.

A halin da ake ciki, ƙasashe daban daban na dunia na ci gaba da kwasar al´umomin su da ke zaune a Labanon.

Nan gaba a yau, za a gana tsakanin Sakatare jannar na Majalisar Dinkin Dunia Koffi Annan, da sakatariyar harakokin wajen Amurika Condolisa Rice, da kuma Sakataren harakokin wajen Kungiyar gamaya turai Havier Solana, domin tantanawa a kan yaƙi tsakanin Labanon da Isra´ila.

Bayanziyara da ya kai jiya a yankin gabas ta tsakiya Havier Solana ya huruci a kan wannan rikici.

Maganar itace ko da mutum zai maida martani da tsokanar da a ka yi masa ya cencenta ya yi wannan martani daidai da dokokin ƙasa da ƙasa, ta yadda ba zai cutawa al´ummomi ba wanda ba su ji ba su gani ba.

Wannan mataki na Isra´ila ba zai taimaka wajen fahintar da jama´aba a kan burin da Isra´ila ke bukatar cimma, na nuna wa dunia cewar Hezbolah annoba ce a rayuwar jama´ar Labanon.

Za a tantanawar, bayan Koffi Annan, ya gana da komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia, domin gabatar masa da rahoto tawagar da majalisar ta aika, a gabas ta tsakiya.

Koffi Annan ya yi kira ga banagrorin2 da su tsaigaita wuta domin ba Majalisar DnkinDu ia damart warware rikicin ta hanyar diplomatia.

Itama ƙungiyar gamayya turai,ta nuna damuwa a game da halin bila´i, da ya rusta da al´ummomin Labanon.

A kan haka, EU ta bada gudunuwar Euro milion 5, don taimakawa jama´ar ƙasar.

Sannan Gamayya turai,ta bada shawara girka wani ziri dominkarbar yan fara hulla da ke shiga gudun hijira.

Kungiyar ta bayana aniyar bada gudunmuwar sojojki a cikin rundunar shiga tsakanin da Majalisar ke shirin aikawa.