1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ɓarin wuta tsakanin dakarun gwamnati da yan tawayen ƙasar Tchad

April 12, 2006
https://p.dw.com/p/Bv28

A kudanci kasar Tchadi, a na ci gaba da barin wuta tsakanin yan tawaye, da dakarun gwamnati.

Yan tawaye sunbayyana samu galaba daga sojojinGwammnati inda su ka kame wasu daga manyan birane kasar, kuma su ke cigaba da darkakawa zuwa N´jamena babban birinin kasar, dominkife gwam,natin shugabanIdriss deby.

Ministan harakokin tsaron Tchadi, Issa Djadallah, ya bayanawa kampanin dullancin labarai na France, cewa a sahiyar yau dakarau masu biyyaya ga gwamnati, sun kwato wasu, daga biranen da ke cikin hannun yan tawaye, to saidai kakakin yan tawayen FUC ,Abdullay Abdulkarim ya mussantan bayananan na ministan tsaro.

Ya tabbatar da cewa, har yanzu,rundunar tawaye, na riƙe da wannan birane, kuma ta na kan hanyar samun nasara shiga birnin N´Djamena.

Ƙasar france, da a yanzu haka, ke da sojoji 1.200, a Tchadi, ta bayyana damuwa, a game da halin da kasar ke ciki.

Wannan saban rikicin tawaye, na wakana a yayin da, a ke cikin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, da za a yi ranar 3 ga wata mai kamawa.

Shugaba mai ci yanzu, Idriss Deby Itino, na daga jerin yan takara.

Yan tawaye sun sha alwashin kiffar da shi, kamin ranar zaɓen.